Bangaren siyasa da zamantakewa;a wani zama na musamman a babban masallacin Suleiman da ke birnin Kazan fadar mulkin kasar ta Tataristan an gudanar da bincike kan matsayin iyali a musulunci da kuma yadda ake kula da lamarin day a shafi iyali musulmi a wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a wani zama na musamman a babban masallacin Suleiman da ke birnin Kazan fadar mulkin kasar ta Tataristan an gudanar da bincike kan matsayin iyali a musulunci da kuma yadda ake kula da lamarin day a shafi iyali musulmi a wannan kasa. A wajan wannan taron an samu halartar iyalai musulmai masu yawa kuma dam asana da malaman addini da masu nazari kan harkokin addini a ranar hudu ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kuma mahalarta wannan taron sun ji dadi da gamsuwa kan yadda a ka gudanar da wannan taro da kuma bayanai masu gamsarwa da aka gabata a gurin wannan taron musamman yadda aka gabatar da ayoyi kur'ani mai girma da hadisai da ke bayani kan rayuwar iyalai.
994185