IQNA

An Kaddamar Da Tarjamar Kur'ani Ta Farko A Cikin Harshen Faransanci A Aljeriya

18:11 - April 30, 2012
Lambar Labari: 2315425
Bangaren kasa da kasa; ma'aikatar harkokin addini da sauran shagulgulan addini a kasar Aljeriya ta kaddamar da wani shiri na tarjama kur'ani mai girma a cikin harshen Faransanci kuma wannan shi ne karon farko da aka kaddamar da wannan shiri kamar yadda kakakin ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a kasar ya bada labara.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ma'aikatar harkokin addini da sauran shagulgulan addini a kasar Aljeriya ta kaddamar da wani shiri na tarjama kur'ani mai girma a cikin harshen Faransanci kuma wannan shi ne karon farko da aka kaddamar da wannan shiri kamar yadda kakakin ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a kasar ya bada labara.Burin wannan shiri dais hi ne fassara kur'ani mai girma cikin tarjama mai inganci da kuma hakan zai bawa wadanda ba larabawa ba kamar masu jin harshen Faransanci karanta kur'ani a cikin fassarar Faransanci ya kuma taimaka masu sanin kur'ani mai girma cikin sauki.
995661
captcha