IQNA

Babban Kur'ani Na Ma'aikatar Kula Da Addini A Masar An sace Shi

17:06 - May 06, 2012
Lambar Labari: 2319685
Bangaren kasa da kasa: wata majiya ta kusa da ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin musulunci a kasar Masar ta bada labarin sace kur'ani mai fi girma a wannan ma'aikatar.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wata majiya ta kusa da ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin musulunci a kasar Masar ta bada labarin sace kur'ani mai fi girma a wannan ma'aikatar. Shi dai wannan kur'ani mafi girma da ke a wannan ma'aikata wata kyauta c eta musamman aka bawa wannan ma'aikata kuma ana ajiye das hi a cikin wannan gini kafin wasu dab a a san ko suwane bas u sace shi. A tab akin wannan majiya wasu ne dab a a san ko suwane ba bayan sun karya makullin kofar ginin na ma'aikatar sai suka shi ofishin ministan ma'aiaktar mai kula da harkokin addini inda suka sace da yin tafiyarsu da wannan kur'ani. Ko dai ba komi wannan wani abin kumya da ciza yatsa ne a ce wani ya tashi takanas ya tafi yin satar kur'ani mai girma musamman a kasa mai cike da tarihi da ci gaban ilimi da addini kasa kamar Masar.
1000248
captcha