Bangaren kasa da kasa; a wani taron manema labarai da aka gudanar kan rawar da mahardata kur'ani mai girma ke takawa a lamuran da suka shafi ci gaban zamantakewa a tsakanin kasashen Chadi da kamaru an bayyana cewa daga farkon daya zuwa hudu ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya da muke ciki a garin Injamaena za a gudanar da taron kan wannan lamari.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a wani taron manema labarai da aka gudanar kan rawar da mahardata kur'ani mai girma ke takawa a lamuran da suka shafi ci gaban zamantakewa a tsakanin kasashen Chadi da kamaru an bayyana cewa daga farkon daya zuwa hudu ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya da muke ciki a garin Injamaena za a gudanar da taron kan wannan lamari.Majiyar labarai ta Asesko da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ne ta watsa rahoton cewa;'wanna taron karawa juna sani da hukumar yada ilimi da al'adu ta Asesko da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta shirya tare da taimakon hadin guiwar kungiyar da ke kula da maharta kur'ani mai girma a duniya ta jami'ar Malik Fahad za a gudanar das hi ne a wannan karo a birnin Injamena fadar mulkin kasar Chadi. A wajan wannan taron kimanin masana da wakilan cibiyoyin da kungiyoyi masu kula da mahardata kur'ani mai girma daga kasashen Kamaru da Chadi za su halarta kuma su yi nazari kan dangataka da rawar da mahardata kur'ani mai girma ke takawa a ci gaban day a shafi zamantakewar kasashen Afrika.
1004990