Bangaren kasa da kasa; a sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar da kuma wadda mu'assisar gudanar da ayyukan da suka shafi bincike da nazarin jin ra'ayin jama'a ta PEW a kasar Amerika ta fitar yayi nuni da cewa: kaso satin da shida cikin dari na al'ummar kasar masar sun bukaci kafa gwamnati da dokokinta suka dogara da asasin koyarwa ta kur'ani da addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar da kuma wadda mu'assisar gudanar da ayyukan da suka shafi bincike da nazarin jin ra'ayin jama'a ta PEW a kasar Amerika ta fitar yayi nuni da cewa: kaso satin da shida cikin dari na al'ummar kasar masar sun bukaci kafa gwamnati da dokokinta suka dogara da asasin koyarwa ta kur'ani da addinin musulunci. Wannan sakamako yana nuni da muhimmancin da kuma rikon da mafi yawa daga cikin al'ummar kasar Masar suke yin riko da addinin musulunci da kur'ani da kuma hatta a fage da dandali na siyasa da makomar kasarsu suna fatar ganin sun zabi jam'iya da mahukumta da za su jagoranci kasa da lamura da harkokin kasarsu kama daga siyasa,tattalin arziki,tsaro,al'ada da zamantakewrsu kasa da al'umma da dai sauran lamura ga mutanan da suka yarda da aiki da tushe na addinin musulunci da kuma yinkoyi da koyarwa irin ta addinin musulunci .Wasu kaso goma cikin al'ummar kasar ta Masar sun bukaci ai aiki da shari'ar musulunci a cikin dokokin da za su tafiayr ad aksar da kuma sabon kudin mulkin da ake son aiwatarwa a kasar a nan gaba.
1006045