IQNA

Yan makaranta Musulmi A Burkina Sun Nuna Adawarsu Da Hana Sanya Hijabi A Guraren Koyarwa

Bangaren kasa da kasa; yan makaranta musulmi a kasar Burkina Faso da ke yammacin Afrika sun aike da wata wasika ga ministan da ke kula da harkokin da suka shafi zamantakewar al'ummar kasar inda a cikin wasikar suke kokawa da nuna adawarsu da yadda wasu daga cikin masu kula da harkokin koyarwa a kasar suke nuna zakewa da yin shisshigi a harkokin da suka shafi koyarwa da take hakkokin dalibai na hana mata musulmi sanya hijibi a gurare da cibiyoyi na koyarwa.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci taIran ne ya watsa rahoton cewa: yan makaranta musulmi a kasar Burkina Faso da ke yammacin Afrika sun aike da wata wasika ga ministan da ke kula da harkokin da suka shafi zamantakewar al'ummar kasar inda a cikin wasikar suke kokawa da nuna adawarsu da yadda wasu daga cikin masu kula da harkokin koyarwa a kasar suke nuna zakewa da yin shisshigi a harkokin da suka shafi koyarwa da take hakkokin dalibai na hana mata musulmi sanya hijibi a gurare da cibiyoyi na koyarwa.majiyar labarai ta lefaso ta watsa rahoton cewa: wani bangare na wannan wasika na shaidawa ministan kula da harkokin da suka shafi zamnatakewar al'ummar kasar ta Burkina Faso inda suka fito fili karara suka bayyana cewa: duk cewa akwai doka kara a cikin kundin tsarin mulkin kasar da ta bada yancin sanya sutura da yancin bayani a kasar amma sai gashi mutanan kasar da ke sanye da suturar musulunci ana takura masu da hana su shiga gurare da cibiyoyi na ilimi da na koyarwa da kuma hana su shiga jarrabawa saboda kawai suna sanye da hijabi kuma a cikin wasikar sun kara da cewa kayan da suturar da suke sanye das u bata hana a gane ko suwane ba ko sauya masu sutura da kasa gane su don haka bas u ga dalilin da za a hana su shiga daki da gurin jarrabawa ba.
1012823