IQNA

Yan Jami'a Musulmi Na Bincike Da Nazari Na Matsayin Rasha Wajen Tabbatar Da Sulhu

Bangaren siyasa da zamnatakewa: bincike da nazari kan matsayi da rawar da kasar Rasha ke takawa wajan tabbatar da sulhu da kwanciyar hankalin al'ummomi da kasashe a fadin duniya a yau kuma yan jami'o'I musulmi da kuma cibiyoyi da mu'assishin koyarwa na koli na musulmi a kasar Rasha suke gudanar da wannan bincike.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci taIran ne ya watsa rahoton cewa: bincike da nazari kan matsayi da rawar da kasar Rasha ke takawa wajan tabbatar da sulhu da kwanciyar hankalin al'ummomi da kasashe a fadin duniya a yau kuma yan jami'o'I musulmi da kuma cibiyoyi da mu'assishin koyarwa na koli na musulmi a kasar Rasha suke gudanar da wannan bincike.Kuma tun ranar ashirin da tara ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya yan jami'ar musulmi da suka fito daga kasar ta Rasha da sauran kasashe suka gudanar da wannan taron bincike da nazari kan rawar da kasar Rasha ke takawa a yau ta fuskar tabbatar da tsaro da sulhu da kwanciyar hankali a duniya . Kuma mahalarta wannan taro sun yi imani da hadewa guri guda cewa a yau kasar rasha tana taka rawar gani wajan tabbatar da sulhu da kwanciyar hankali a kokarin magance matsaloli da kasashen duniya ke fuskanta a wannan fanno musamman idan aka yi la'akari da yadda ake fuskantar zalunci da danniya da babakewa da bakar siyasa daga wasu kasashen kamar Amerika da kasashen yammacin turai da wasu yan koransu a yankin gabas ta tsakiya da sauran kasashe da nahiyoyi na duniya.

1012580