IQNA

Gasar Kur'ani Ta Kasa Da Kasa A Tsakanin Yan Jami'a Wani sauyi Na Na Al'ada

13:04 - May 23, 2012
Lambar Labari: 2332512
Bangaren da ke kula da harkokin kur'ani: mai kula da shirya gasar karatun kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran yayi nunida shirya gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a tsakanin yan jami'a musulmi da cewa: ta hanyar gudanar da irin wannan gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a tsakanin yan jami'a musulmi muna iya samar da wani juyin juya halinm na al'adu a tsakanin yan jami'a.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mai kula da shirya gasar karatun kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran yayi nunida shirya gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a tsakanin yan jami'a musulmi da cewa: ta hanyar gudanar da irin wannan gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a tsakanin yan jami'a musulmi muna iya samar da wani juyin juya halinm na al'adu a tsakanin yan jami'a.Habib Mahki a wata tattauanawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labarai na Ikna kan yadda ake gudanar da shirye shirye na gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa a tsakanin yan jami'a musulmi karo na hudu ya bayyana cewa;wannan gasar wata alama ce da ke nuni da yadda harkar da ta shafi karatun kur'ani mai girma ta fara zama da gindinta a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya ci gaba da bayyana cewa: a ganinsa a tsawon shekarun juyin juya halin musulunci a nan jamhuriyar musulunci yan jami'a sun taka rawar gani a gasar karatun kur'ani a cikin iran ko a matakin kasa da kasa tafuskar adadi ko inganci .
1013045
captcha