IQNA

Zaman Taro Kan Ci gaban Al’adun Iran Da Na Musulunci A Kasar Italia

Bangaren al’adu da fasaha, an gudanar da zaman tattaunawa kan ci gaban al’adun Iran da na muslunci a babbar cibiyar bincike da ke gabacin birnin Rom fadar mulkin kasar Italia tare da halartar masana daga kasashen biyu wadanda suka gabatar da laccoci da kuma kasidu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu cewa an gudanar da zaman tattaunawa kan ci gaban al’adun Iran da na muslunci a babbar cibiyar bincike da ke gabacin birnin Rom fadar mulkin kasar Italia tare da halartar masana daga kasashen biyu, inda tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi tarihin Iran da kuma n muslunci.
Zaman taron dai ya zo a kokarin da kasashen biyu suke yi wajen ganin sun bude wani sabon shafi ta fuskar bunkasa harkokin al’adu, kasantuwarsu tsoffin dauloli da suka shahara a tarihi tsawon dubban shekaru da suka gabata, wanda kuma suka samu canji a dukaknin bangarori kama daga siysa da kuma akida da al’adu da suke da dangantaka da addinina da suke bi daga bisani bayan samun sauyi a cikin tafiyarsu.
an gudanar da zaman tattaunawa kan ci gaban al’adun Iran da na muslunci a babbar cibiyar bincike da ke gabacin birnin Rom fadar mulkin kasar Italia tare da halartar masana daga kasashen biyu wadanda suka gabatar da laccoci da kuma kasidu da suka shirya domin zaman taron.
Daga karshe dai dukaknin bangarorin biyu sun cimma matsaya kan ci gaba da gudanar da irin wannan taro lokaci zuwa lokaci a mabnbantan wurare, domin tabbatar da cewa an kara fitar da abubuwa da suka shafi al’adun al’ummomin biyu. 1014811