IQNA

An Gudanar Da Taron Baje Koli Na Littafai Na Kasa Da Kasa A Ukraine

Bangaren al’adu da fasaha, an gudanar da taron aje koli karo na takwas a kasar Ukraine na littafai a matsayi na kasa da kasa tare da halartar cibiyoyi da madaba’antu akalla 200 daga cikin gidan da ma wajen aksar da suka halarci wannan bababn taro na baje kolin littafai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da taron aje koli karo na takwas a kasar Ukraine na littafai a matsayi na kasa da kasa tare da halartar cibiyoyi da madaba’antu akalla 200 daga cikin gidan da ma wajen aksar da suka halarci wannan bababn taro na baje kolin littafai na duniya.
A wani labarin makamancin wannan an fara gudanar da taron baje koli na littfai a matsayi na duniya a kasar Georgia tare da halartar cibiyoyin buga littafa kimanin saba’in na ciki da waje da suke baje abubuwan da suke bugawa na liffai da sauransu domin amfanin masu nazari na ciki da wajen kasar.
An bude wani ofishin kula da harkokin addini na kasar Kyrgystan a kasar Kuwait da nufin kara bunkasa harkokin addini da kuma kyakyawar alaka tsakanin kasashen ta fuskkar bunksa harkokin addini da ilim ga mi da al’adu a tsakaninsu kasantuwarsu mambobi a cikin kungiyar kasashen musulmi.
A cikin wanmnan makon ne wani mutum da ake kira mai bayar da fatawa na gwamnatin Saudiyya Abdulaziz Bin Abdullah Al-sheikh, ya fitar da wata fatawa daga mahangarsa ta akidar wahabiyanci da ke kafirta musulmi kansu wadanda ba su bin wannan tafarki na wahabiyanci, inda ya halasta kaddamar da kai hare-hare kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista.
1016634