Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: maikel Guvo ministan da ke kula da harkokin da suka shafi ilimi da koyarwa a kasar Britaniya ya bayyana cewa:raba kur'ani a makarantu babu wata matsala musamman da sunan taimakawa wajan yada wannan littafi mai tsarki da yada addini a makarantun.Jaridar Telegraph da ake bugawa a kasar Britaniya c eta nakalto ministan yana amsa tambayar da gidan radiyon BBC ya yi masa cewa shin ta hanyar raraba kur'ani da sauran littafai mai muhimmanci kamar kur'ani a makarantu kuna ganin za ku ci nasara kuwa? Sai ya amsa da cewa; idan shugabanni da darektocin makarantu suka gabatar da bukatar hakan tabbas za mu yi maraba da hakan kuma ma'aikatar ilimi da kula da koyarwa ashirye take a makarantun Britaniya ta bata izinin amfani da littafi mai tsarki na musulmi wato kur'anai kuma wannan zai taimaka wajan samar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin musulmi da sauran wadanda ba musulmi ba. Ya zuwa yanzu an rarraba kur'anai dubu ashirin da hudu a makarantun Britaniya kuma ma'aiaktar da ke kula da koyarwa ta kasar Ta Britaniya tare da taimakon masu bada taimako suka rarraba.
1017502