Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Radifullah cewa an gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Rasha wadda ta samu halartar wakilan cibiyoyin muslunci na kasar da kuma makarantun kur’ani inda aka kammala gasar bayan kwashe kwanaki takwas ana gudanar da ita kafin kammalawa.
Maga takardan hukumar zaben kasar Masar Hatem Bagato, ya nuna cewa korafe-korafen da aka gabatar a zaben shugaban kasar zagaye na farko da ya gudana na iya sauya sakamakon zaben da wasu ke ambatawa a kasar.
Ya ce sakamakon da ake bayyanawa har ya zuwa yanzu ba na dindindin bane, hukumar zaben na cikin nazarin korafe-korafen da aka shigar game da rishin bin ka'idodin zabe, kuma wannan korafi za su iya kawo sauyi a cikin wasu sakamakon zaben, inda ya kara da cewa za su bayyana sakamakon a yau litinin ko gobe talata , bayan sun yi nazarin daukacin korafe-korafen.
Dan takarar da ya zo matsayi na 3 Hamdeen Sabbahi, a ranar sasabar, ya ce zai shigar da kara wajen hukumar zaben game da taka dokoki da kin bin gaskiya lokacin zaben. Sakamakon zaben na ranar 23-24 ga wannan wata da yan uwa musulmi da kafafen yada labarai suka bayyana na cewa, Mohamed Morsi, dan takarar yan uwa musulmi shike kan gaba da wajen 25% ya na biye da Ahmed Chafiq, mai .
Idan dai har hukumar zaben ta tabbatar da wannan sakamako za a je zagaye na biyu tsakanin Mohamed Morsi, da Ahmed Chafiq, a tsakiyar watan Juni, don tattance wanda zai zamanto shugaban kasar ta Masar bayan Hosni Mubarack.
1017758