Bangaren kasa da kasa; hadin guiwar bangaren sha hudu ga watan Fevreru a kasar Bahrain sun jinjinawa Ayatullahi Ali Khamna'I jagoran juyin juya halin musulunci na Iran day a nuna goyan bayansa da masu kokarin ganin an kawo sauyi da canjin yanayi a kasar Baharain.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: hadin guiwar bangaren sha hudu ga watan Fevreru a kasar Bahrain sun jinjinawa Ayatullahi Ali Khamna'I jagoran juyin juya halin musulunci na Iran day a nuna goyan bayansa da masu kokarin ganin an kawo sauyi da canjin yanayi a kasar Baharain. A jogoran juyin juya halin musulunci a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ayatullahi Ali Khamna'I a cikin jawabin day a gabatar a ranar tunawa da zagayowar ranar da imam Khomeini wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran yayi bankwana da wannan duniya ya bayyana cewal; takaicinsa da manyan kasashe masu nuna girman kai da zalunci da kawo banbanci a tsakanin al'ummomi da kasashe suka yi gum da bakinsu bas u cewa uffin kan zaluncin da ake nunawa al'ummar kasar Bahrain masu fafitikar neman kawo sauyi a wannan kasar da kuma yadda suke goyan bayan azzalumar gwamnati da gidan sarautar wannan kasa . A bangare daya ya nuna goyan bayan jmahuriyar musulunci ta Iran da al'ummarta ga mutanan da ake zalunta a kasar ta Bahrain.
1023033