IQNA

Samar Da hadin kai A Tsakanin Musulmi Shi Ne Burin Shirya gasar Karatun Kur'ani A Tsakanin Yan jami'a

15:10 - June 07, 2012
Lambar Labari: 2341656
Bangaren harkokin kur'ani mai girma" mukaddashin ofishin da ke kula harkokinnda suka shafi jami'o'I day an jami'a da kuma bangaren ilimi musamman harkokin da suka shafi kur'ani mai girma ya bayyana cewa: shirya gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa a tsakanin yan jami'o'I na musulmi zai samar da wani yanayi na kara kusantar juna da samar da hadin kai a tsakanin musulmi da suka fito daga kasashe daban daban na duniya kuma wannan shi ne babban burin shirya wannan taron.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi alkur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mukaddashin ofishin da ke kula harkokinnda suka shafi jami'o'I day an jami'a da kuma bangaren ilimi musamman harkokin da suka shafi kur'ani mai girma ya bayyana cewa: shirya gasar karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa a tsakanin yan jami'o'I na musulmi zai samar da wani yanayi na kara kusantar juna da samar da hadin kai a tsakanin musulmi da suka fito daga kasashe daban daban na duniya kuma wannan shi ne babban burin shirya wannan taron.Nasrullah Camram a wata tattauanawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya bayyana haka da kuma ya kara nanatawa da cewa shirya irin wannan gasar musamman ta kur'ani mai girma a tsakanin jami'o'I day an jami'a musulmi zai kara habakawa da himma a kokarin da ake yin a samar da yanayi mai kyau da hadin kai a tsakanin musulmi da kasashensu kuma ko shakka babu irin wannan mataki zai taimaka matuka gaya ta bangarori daban daban.
1023831
captcha