Bangaren harkokin kur'ani :a ranar ashirin da biyu ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya za a gudanar da taron manema labarai dangane da shirya gasar karatun kur'ani mai tsarki karo na ashirin da tara da aka saba gudanarwa a nan jamhuriyar musulunci ta Iran kuma za a samu halartar shugaban riko na hukumar da ke kula da harkokin da suka shafi addini a kasar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi alkur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar ashirin da biyu ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya za a gudanar da taron manema labarai dangane da shirya gasar karatun kur'ani mai tsarki karo na ashirin da tara da aka saba gudanarwa a nan jamhuriyar musulunci ta Iran kuma za a samu halartar shugaban riko na hukumar da ke kula da harkokin da suka shafi addini a kasar. Da misalign karfe goma na safe ne a wannan rana ta ashirin da biyu ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya za a fara gudanarwa a babban dakin taro na shahid Muhlati a hukumar da ke kula da harkokin addini da ken an birnin Tehrain kuma Hujjatul Islam wal musulm Ali Mahammadi wakilin jagoran juyin juya halin musulunci kuma shugaban riko na hukumar ne zai jagoranci wannan taron manema labarai kan shirye shiryen da aka yi tanadi kan wannan gasar ta karatun kur'ani mai girma.
1024336