IQNA

Zaman Taro Na Kara wa Juna Sani Kan Ayyukan Rubutun Kur'ani Mai tsarki

23:05 - June 18, 2012
Lambar Labari: 2349287
Bangaren kur'ani, taron kara wa juna sani kan ayyukan rubutun kur'ani mai tsarki ya fara gudana a fadar mulkin jamhuriyar musulnci da nufin samar da wasu hanyoyi da suka dace domin kara kyautata rubutun kur'ani a matsayin wani aiki na fasa da aka san cibiyoyin buga littafai na musulmi das hi.

Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, taron kara wa juna sani kan ayyukan rubutun kur'ani mai tsarki ya fara gudana a fadar mulkin jamhuriyar musulnci da nufin samar da wasu hanyoyi da suka dace domin kara kyautata rubutun kur'ani a matsayin wani aiki na fasa da aka san cibiyoyin buga littafai na musulmi das hi tsawon zamuna da suka gabata.

A wani rahoton na daban kuma an bayyana cewa, wakilan dan takarar shugabancin kasar Masar na kungiyar ikhwan sun sanar cewa dan takararsu Muhammad Mursi shi ne ya lashe zaben da aka gudanar zagaye na biyu a kasar.
Kakakin Muhammad Mursi Muhamamd Baraka ya fadi a daren jiya cewa an kusan kammala kirgia dukkanin kuri'un da aka kada a zaben, kuma dan takararsu Muhammad Mursi yana kimanin kashi 52.5% na kuri'un, yayin abokin hamayyarsa Ahmad Shafiq yake da kashi 47.5%, wanda hakan a cewarsa ya tabbatar musu da cewa dan karar nasu ne ya lashe zaben.
Bayan fitar da wannan sanarwa da kakakin Mursi ya yi magoya bayan kungiyar ikhwanul muslimin suka yi cincirindo a dandalin Tahrir da ke tsakiya birnin Alkahira domin nuna murna da farin cikinsu, a ranar Alhamis ne za a sanar da sakamakon karshe na zaben na kasar Masar.
1032323


captcha