IQNA

Zaman Taro Domin Nazari Kan Matsayin Imam Musa Kazim (AS) A ranar Shahadarsa

Bangaren fikira da ilimi, an gudanar da zaman taro domin nazari kan rayuwar Imam Musa Kazim (AS) a husainiyar Bakiyyatul da ke garin Zaria wanda yan kungiyar harkar muslunci suka dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karon farko.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da zaman taro domin nazari kan rayuwar Imam Musa Kazim (AS) a husainiyar Bakiyyatul da ke garin Zaria wanda yan kungiyar harkar muslunci suka dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a karon farko tare da halartar malaman addinin muslunci da kuma masana daga jami’oi na kasar.

malamin addinin musluncin nan na kasar Tunisia Tijani Samawi ya bayyana cewa Imam Shahid Bakir Sadr baya ga cewa shi ne mutum na farko a cikin larabawa da ya fara fitar da tunain mikewar al’ummar larabawa domin kalubalantar azzaluman shugabanninsu, shi ne kuma mutumin da ya kalubaanci zalunci dawagitan Iraki ba tare da wani shayi ba.
Mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbat a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a kasar Filland tare da halartar malaman addini da kuma masana daga sassan kasar musamman ma wakilan cibiyoyin addini muslunci masu zaman kansu.

ofishin shugaban kasar Tunisia ya fitar da wani bayani da acikinsa yake bayyana cewa yin wasu kalamai na keta alfarmar addinin muslunci ba shi ne ma’anar fadin albarkacin baki ba kamar yadda wasu suka dauka kuma suke amfani da wannan damar domin cin zarafin musulmi a cikin kasar da ma wajenta.
Baynain ya ce dole kowa ya girmama addinin kowane bangare a cikin dokokin kasar Tunisia, musulmi ba shi da hakkin ya ci zarafin wani saboda shi ba musulmi ba ne, kamar yadda wani wanda ba musulmi ba ba shi da ahhaki ko hurumin cin zarafin muslmi, haka nan kuma ko da musulmin ne ba shi da hakkin ya yi kalaman batunci kan akidar musulmci saboda wasu ra’yoyi nasa, yin hakan ya saba ma kundin tsarin mulki.
1034433