Bangaren kur’ani, ganawar jagoran juyin juya halin musulunci tare da jami’ai da suka dauki nauyin shiryawa da gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya karo na 29 gami da alkalan gasar da suka ziyarce shia gidansa domin ganawa da shi da kuma jin bayanansa kan gasar da irin sakon da yake dauke da shi ga duniyar musulmi kan hakan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da ganawa da jagoran juyin juya halin musulunci tare da jami’ai da suka dauki nauyin shiryawa da gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya karo na 29 gami da alkalan gasar da suka ziyarce shia gidansa domin ganawa da shi da kuma jin bayanansa kan gasar da irin sakon da yake dauke da shi ga duniyar musulmi kan hakan kamar dai yadda ya saba yi a kowace shekara.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci sallar juma'ar birnin Tehran inda a hudubobin day a gabatar ya tabo lamurra masu muhimancin gaske da suka shafi duniyar musulmi da kuma sauyin da ake samu a duniya, lamarin da ya janyo kuma yake ci gaba da janyo hankulan kafafen watsa labarai na duniya. Jin kadan bayan kare hudubar kafafen watsa labarai na duniya suka fara watsawa da kuma yin sharhi kan abubuwan da hudubar ta kumsa.
A nasa bangaren kamfanin dillancin labaran Reuters ya fi ba da muhimmanci ne ga martanin Jagoran kan barazanar takunkumi da harin soji da wasu kasashe suke yi wa Iran din inda ya ce jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce ko da wasa Iran ba za ta taba mika kai ga matsin lambar da kasashen yammaci suke mata ba wajen ganin ta dakatar da shirin nukiliyanta ba. Kamfanin dillancin labaran ya ci gaba da rubuta cewa Ayatullah Khamenei ya ce takunkumin da aka sanya wa Iran ba zai yi wani tasiri a kan kudurin kasar Iran a wannan fage na nukiliya ba, kamar yadda kuma ya mayar da martani ga Amurka da kawayenta da suke wa Iran din barazanar sanya mata takunkumi da kuma kawo mata harin soji da cewa Iran ma tana da irin nata barazanar wacce za ta yi hakan a duk lokacin da ta ga ya dace. Kamar yadda kuma kamfanin Reuters din kawo bangaren da Jagoran ya jaddada cewar Iran za ta taimakawa duk wata al'umma ko kuma kungiyar da take fada da hki ba tare da wani noke-noke ba.
Shi ma kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya fi ba wa bangaren jawabin Jagoran da ya mayar da martani kan kasashen da suke wa Iran din barazana da takunkumi da kawo harin soji da cewa Iran za ta mayar da martani kan hakan da dukkan karfinta. Shi kuwa kamfanin Associated Press na Amurka ya fi ba da muhimmanci ne ga bangaren da Jagora ya yi magana kan HKI da bayyana ta a matsayin cutar kansar da wajibi ne a kawar da ita, da kuma cewa Iran za ta goyi bayan duk wata al'umma ko kungiyar da ta ke son fada da gwamnatin yahudawan sahyuniya.
1036824