Bangaren kur’ani, minista mai kula da harkokin addinin muslunci a kasar Philipines ya bukaci a kara fadada alaka da jamhuriyar muslunci ta Iran musamman ma a bangarorin da suka shafi karatun kur’ani mai tsarki ta yadda hakan zai taimaka musu matuka wajen kara habbaka lamurran kur’ani mai tsarki a kasar tasu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na cibiyar bunkasa harkokin ilimi da ala’du cewa minista mai kula da harkokin addinin muslunci a kasar Philipines ya bukaci a kara fadada alaka da jamhuriyar muslunci ta Iran musamman ma a bangarorin da suka shafi karatun kur’ani mai tsarki ta yadda hakan zai taimaka musu matuka wajen kara habbaka lamurran kur’ani mai tsarki a kasar tasu wadda adadin musulmi ke ci gaba da karuwa acikinta.
shugaban kwamitin amintattu na majalisar malaman kasar Bahrain Ahmad Zain ya sheda cewa shigar da sojojin mamayar kasar saudiyya suka yia acikin kasar Bahrain domin murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana da neman hakkokinsu da aka haramta musu ya yi hannun riga da dukaknin dokokin kasa da kasa, da ma dokokin kasar ta Bahrain.
A bangare guda kuma kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin kasar.
Bayanin kungiyar ya ci gaba da cewa: Zanga-zangar ranar alhamis din da ta gabata an yi ta ne domin kira da a saki fursunonin siyasa da ake tsare da su da kuma kawo karshen wariyar da ake yi wa 'yan shi'a a yankin, a cikin watannin bayan nan dai jami'an tsaron Saudiyya sun rika bude wuta akan masu zanga-zangar lumana da su ke son a samar sa sauye-sauye na siyasa a cikin kasar wadda keda kashin ashirin cikin dari na mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah.
1036252