Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz cewa, daya daga cikin fitattaun malamai da suka daukar nauyin shirya gasar kur'ani ya bayyana cewa, irin yadda mutane masu bin tafarkin addinin muslunci suke karbar gasar karatu da harder kur'ani da ake gudanarwa ya tabbatar da cewa makiya bas u nasara a kan manufofinsu na dusashe hasken kur'ani mai tsarkia acikin zukatan musumi da sauran al'ummomin duniya ba, domin kuwa duk wata shiriya da hannuka mai sanda dad an adam zai samu na cikin kur'ani mai tsarki.
A jiya lahadi, gwamnatin kasar Tunisiya ta tusa keyar tsofon fraministan kasar Libiya zamanin milkin Khadafi Al-Bagdadi Al-Mahmudi, zuwa birnin Tripoli fadar milkin kasar Libiya, cikin wani gaggawa, inda aka ci gaba da tsare shi.
Wannan mataki na iya kawo sabani mai girma a cikin gida tsakanin gwamnati da shugaban kasar da bai bada ba amincewarsa a matakin. Mahmudi mai shekaru 67 na tsare ne a kasar Tunisiya tun ranar 21 ga watan Septemba. Bayan an karbe shi fraministan gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Libiya Abdel Rahim Al-Kib, ya ce za a tsrae shi tamkar yanda addini ya koyar kamar yanda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Lauyan dake kare shi Mabruk Kourchid, ya ce wannan mataki da kasar Tunisiya ta dauka ya saba ma dokoki da kudirori na hakkin bil Adama, kuma babbar matsalar it ace shugaban kasar Tunisiya bay a da labara game da wannan mataki. Da farko shugaban kasar Tunisiya Moncef Marzouki, ya bayyana rishin amincewarsa ga matakin maika Al-Mahamudi ga gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Libiya tare da bukatar samun tabbaci daga kasar ta Libiya game da mutunta hakkokin dan Adam, amma shugaban gwamnatin Tunisiya Hamadi Jebali ya ce ba za a ci tuwon fashi ba game da maika shi.
1037034