IQNA

Gasar Karatun Kur'ani Mai Tsarki Dole Ta Zama mai Yin Tasiri A Cikin Mutane

17:53 - June 26, 2012
Lambar Labari: 2355189
Bangaren kur'ani, da dama daga cikin mahalarta gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki sun jadda muhimmancin saka gasar karatu da harder kur'ani ta zama mai tasiri a cikin rayuwar zamantakewar mutane maimakon takaituwa kawai da karatun kuma a gaban jama'a ko samun myautuka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, da dama daga cikin mahalarta gasar karatu da harder kur'ani mai tsarki sun jadda muhimmancin saka gasar karatu da harder kur'ani ta zama mai tasiri a cikin rayuwar zamantakewar mutane maimakon takaituwa kawai da karatun kuma a gaban jama'a ko samun myautuka kamar dai yadda suka hadu a kan hakan.
Duk wanda ya ke bin siyasar kasar Saudiyyan ya san irin gasar neman mulki da ke gudana tsakanin ‘ya'yan gidan sarautar Al Sa'ud musamman bayan mutuwar tsohon yarima mai jiran gadon wato Yarima Sultan a watan Oktoban bara inda gasar ta fito fili tsakanin masu neman wannan sarautar. Irin wannan yanayi ne yake sanya kasar Saudiyya cikin yanayi na dar-dar a duk lokacin da batun nadin sarki ko yarima mai jiran gado ya taso musamman idan aka yi la'akari da cewa su al'ummar kasar ba su da bakin Magana cikin wannan nadin.
A dabi'ance dai sarki Abdullah shi ne ya ke da alhakin nada sabon yarima mai jiran gadon, sannan kuma kasar Saudiyya sabanin sauran kasashen larabawa masu mulkin kama-karya na sarakuna ana musayen mulkin ne tsakanin ‘yan'uwa (wa da kani) sabanin sauran kasashen inda da ne ya kan gaji mahaifinsa, irin wannan yanayin ma ya sanya Saudiyyan cikin damuwa bisa la'akari da tsufan da sauran ‘ya'yan Abdul'aziz kannen sarkin Abdullah suka yi wanda ake ganin matukar dai suka ci gaba da rike mulki to za a ci gaba da samun irin wannan yanayi na mutuwa da musayen mulki daga wanann zuwa wancan. A halin yanzu dai mutumin da ake ganin daga dukkanin alamu shi ne zai dare wannan matsayi na yarima mai jiran gado shi ne Yarima Salma shi ma kansa ya ba wa shekaru 70 baya sannan ga kuma rashin lafiyar da yake fama da ita. A saboda haka ne wasu suke ganin ba wa mutum mai irin wadannan shekaru da kuma yanayi na rashin lafiya wanann matsayi lamari ne da ke cike da hatsari da kuma yiyuwar faruwar abin da ya faru a baya na yadda yarima mai jiran gadon da ya mutun bai wuce watanni 8 a wannan karagar mulki ba. Irin wannan yanayin ne ya sanya su ma jikokin Abdul'aziz din mikewa da kokarin bayyanar da kansu don rike wanann matsayi musamman rahotannin da suke nuni da kokarin da sarki Abdullahin ya ke na nada dansa a wannan matsayi.
Wani lamarin kuma da ke da muhimmanci a lura da shi a wannan bangaren shi ne rawar da wasu kasashen waje musamman Amurka za ta taka wajen nada sabon yarima mai jiran gadon saboda muhimmancin da Saudiyyan take da shi a wajensu musamman idan aka yi la'akari da siyasar yarima Nayef din a ciki da wajen kasar Saudiyya wacce ko kai tsaye ko ta wata hanya ta yi daidai da wasu daga cikin siyasr Amurkan musamman siyasarsa ta fada da duk wani kokarin kawo sauyi da neman ‘yancin kai na hakika a kasar Saudiyyar da ma sauran kasashen larabawa da kuma kiyayyar da yake yi da kasashe masu adawa da Amurkan irin su jamhuriyar Musulunci ta Iran.
1032995

captcha