Bangaren kur’ani, wasu daga cikin alkalan gasar karatun kur’ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Tehran karo na 29 sun yi amanar cewa yanayin karatun ‘yan kasashen ketare da suka halarci gasar ya sha banbam da lokutan baya musamman ta fuskar kyautata karatu sauti inda kawai suka fi ba kaidojin karatu muhimamnci a yayain gasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, da dama daga cikin alkalan gasar karatun kur’ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Tehran karo na 29 sun yi amanar cewa yanayin karatun ‘yan kasashen ketare da suka halarci gasar ya sha banbam da lokutan baya musamman ta fuskar kyautata karatu sauti inda kawai suka fi ba kaidojin karatu muhimamnci a yayain gasar duk kuwa da cewa na kokarin kamanta karatukansu da makaranta na Masar.
Za a gudanar da wani zaman taro domin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya ddinin muslunci da kuma mabiya addinin kiristanci da ma sauran addinai a birnin London na kasar Birtaniya tare da halartar malamai da masana daga sassa na kasar da ma wasu kasashen ketare.
Wannan zaman taro yana daya daga cikin muhimamn taruka da kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu na muslunci ke shirin shiryawa abirnin na London, kuma ya samu karbuwa daga mutane da dama da aka aike musu da goron gayyatar halartar taron, musamman ma masana da malaman addinin muslunci na kasar da kuma wasu kasashen musulmi da na larabawa.
Gudanar da wani zaman taro domin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya ddinin muslunci da kuma mabiya addinin kiristanci da ma sauran addinai a birnin London na kasar.
1040724