IQNA

Shekaru Takwas Kenan Da Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya Ta Haramta Katangar Wariya

13:36 - July 16, 2012
Lambar Labari: 2369900
Bangaren kasa da kasa, kimanin shekaru takwas kenan da kotun manyan laifuka ta duniya ta sanr da cewa katangar wariya da haramtacciyar kasar Isra'ila ta gina a cikin yankunan palastinawa marassa kariya ba tare da kasashen duniya sun ce uffan a kansa ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Ilsma Time cewa, kimanin shekaru takwas kenan da kotun manyan laifuka ta duniya ta sanr da cewa katangar wariya da haramtacciyar kasar Isra'ila ta gina a cikin yankunan palastinawa marassa kariya ba tare da kasashen duniya sun ce uffan a kansa ba saboda lamari ne da ya shafi yahudawan sahyuniya.
Bayan jerin kisan gillan da aka yi wa wasu daga cikin masanan nukiliyan kasar Iran da kuma bayanan da jami'an tsaron kasar suka fitar da ke nuni da hannun cikin hakan bayanai suke ci gaba da fitowa da suke tabbatar da wannan ikirari na Iran din. Bayani na baya-bayan nan shi ne wanda dan jaridar tashar talabijin din nan na Amurka Dan Raviv da kuma Yossi Melman wanda shi ma dan jarida ne a suka fitar cikin wani sabon littafi da suka buga mai sunan 'Spies Against Armageddon' inda a cikin littafin suka yi karin haske dangane da hannun da HKI take da shi wajen kisan gillan da aka yi wa masanan na Iran cikin 'yan shekarun nan.
A wata tattaunawa da ya yi da tashar din, Dan Raviv ya bayyana cewar a cikin kungiyar leken asirin akwai wani bangare da aka ware da aka ba su aikin kashe masanan nukiliyan Iran. Har ila yau a cikin wannan littafin, marubucin ya yi ishara da wasu daga cikin ayyukan ta'addanci da kisan gilla da kungiyar din ta aikata a biranen Beirut da Damaskus na kasashen Labanon da Siriya inda yake cewa a halin yanzu 'yan kungiyar leken asirin Amurka da HKI suna aiki tare wajen ganin sun dakatar da shirin nukiliyan. Daga cikin ayyukan da suke gudanarwa tare da har da aiko da 'virus' zuwa ga kwamfutocin cibiyoyin nukiliyan na Iran da kuma ci gaba da tattaro bayanai kan masanan na Iran.
Dangane da wannan batu na aiko da kwayoyin cutar kwamfuta irin su Stuxnet da Flame zuwa ga kwamfutocin cibiyoyin nukiliyan Iran, marubucin ya bayyana cewar: cibiyar leken asirin soji ta HKI da kuma kungiyar leken asirin cikin gida ta Amurka NSI sune suka kirkiro wadannan virus din da nufin lalata kwamfutocin da kuma tattaro bayanan sirri da suke cikinsu.

1053118
captcha