IQNA

Musawi Ya Nuna Kwazo Matuka A Gasar Karatun Kur’ani Ta Tashar Alkausar

22:43 - August 16, 2012
Lambar Labari: 2394560
Bnagaren kasa da kasa, musawi marakncin kur’ani mai tsarki dan kasar Iran ya taka gagarumar rawa tare da nuna kwazo matuka a gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Iran da ake gabatarwa a cikin wannan wata na ramadan mai alfarma da ake watsawa kai tsaye.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa Mahmud Jawad musawi marakncin kur’ani mai tsarki dan kasar Iran ya taka gagarumar rawa tare da nuna kwazo matuka a gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Iran da ake gabatarwa a cikin wannan wata na ramadan mai alfarma da ake watsawa kai tsaye a talabijin din.
A wani labarin kuma za a gudanar da wata gasa ta bincike kan sanin addinin muslunci wato akidarsa dakuma abubuwan da yake koyarwa daidai da abin da ke cikin littafin kur’ani mai tsarki da kuma koyarwar manzon musulunci tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka wanda za a kammala amsar sakamakon a birnin Kiev.
an gudanar da taron aje koli karo na takwas a kasar Ukraine na littafai a matsayi na kasa da kasa tare da halartar cibiyoyi da madaba’antu akalla 200 daga cikin gidan da ma wajen aksar da suka halarci wannan bababn taro na baje kolin littafai na duniya.
A wani labarin makamancin wannan an fara gudanar da taron baje koli na littfai a matsayi na duniya a kasar Georgia tare da halartar cibiyoyin buga littafa kimanin saba’in na ciki da waje da suke baje abubuwan da suke bugawa na liffai da sauransu domin amfanin masu nazari na ciki da wajen kasar. 1079226
captcha