IQNA

An Kai Harin Ta'addanci A Hubbaren Muhsin Bin Hussain (AS)

10:34 - August 26, 2012
Lambar Labari: 2398858
Bangaren kasa da kasa, wasu yan ta'adda sun kai wani hari a hubbaren Muhsin dan Imam Hussain (AS) da ke garin Halab na kasar Syria inda suka tarwatsa wurin da bama-bamai a wani mataki na fara kaddamar da harin ta'addanci kan wurare masu tsarki da ke yankin.




Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa wasu yan ta'adda sun kai wani hari a hubbaren Muhsin dan Imam Hussain (AS) da ke garin Halab na kasar Syria inda suka tarwatsa wurin da bama-bamai a wani mataki na fara kaddamar da harin ta'addanci kan wurare masu tsarki da ke yankin kamar yadda suke a cikin kasar Iraki.

A daya bangare kuma sabon Manzon da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Kasashen Larabawa ke shirin turawa zuwa kasar Siriya Lakhdar Brahimi, ya ce ya yi murna da karamcin da aka yi masa ta hanyar nada shi a kan wannan matsayi, to amma kuma yana cikin damuwa da kuma shakku dangane da irin kuncin da ke tattare da aiki da ke gabansa. Brahimi ya bayyana hakan ne a yammacin jiya lokacin da yake ganawa da Babban Magakatarda na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon a birnin New York kafin ya gana da sauran jakadojin kasashen duniya da ke Majalisar ta Dinkin Duniya.

To sai dai ya ce abu mafi muhimmaci a gare shi shi ne al'ummar kasar Siriya amma ba nuna bangaranci ko kuma son-kai a cikin aikinsa ba. Ita dai gwamnatin kasar Siriya ta bakin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Faysal Meqdad, ta ce tuni ta sanar da Majalisar Dinkin Duniya a rubuce cewa, za ta bayar da cikakken hadin-kai ga sabon Manzon nata Lakhdar Brahimi kamar dai yadda ta bai wa wadanda suka gabace shi hadin-kai.

1083990
captcha