IQNA

Yin Amfani Da Kungiyar Larabawa Da Yan ba Ruwanmu Wajen Warware matsalolin Yanki

22:00 - August 31, 2012
Lambar Labari: 2402202
Bangaren siyasa, taron kungiyar kasashen yan ba ruwanmu wata babbar dama ce da ya kamata a yi amfani da ita wajen warware batutuwa da dama na yankin gabas ta tsakiya kasantuwar dukkanin kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen larabawa suna ciki kamar kungiyoyi na kasashen duniya da dama suna ciki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a lokacin da yake ganawa da pira mistan Iraki jagora ya bayyana cewa taron kungiyar kasashen yan ba ruwanmu wata babbar dama ce da ya kamata a yi amfani da ita wajen warware batutuwa da dama na yankin gabas ta tsakiya kasantuwar dukkanin kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen larabawa suna ciki kamar kungiyoyi na kasashen duniya da dama suna cikin wannan kungiya.
Jagoran juyin juya cewa, Kasar Iran na gamsuwa da yanda matsayi da karfi da darajar kasar Iraki, ke bunkasa yau da gobe a cikin duniyar larabawa da musulmi, inji jagoran juyin juya halin musulumci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, yayi wannan furuci ne jiya litinin yayin da ya gana da praministan kasar ta Iraki Nuri Almaliki, da ya kawo wata ziyara a nan Teheran.
Jagoran ya kara da cewa, kokarin da zai taimaka wajen kara tabbatar da karfin magabatan kasar ta Iraki, musamman game da jihadi na kimiya hade da ayukan sake gina kasar, sune za su habbaka matsayin kasar da cimma guri da bukatun al'ummar kasar da ma gwamnatin kasar baki daya. Inda ya nuna cewar irin abubuwan da suka gudana a cikin kasar a yan watannin nan, sun farkar da gwamnati da al'ummar kasar game da irin matsayi da kuma rawar da za su iya takawa a cikin duniyar larabawa da musulmi.
A mahangar jagoran juyyin juyya halin musulumci, fucewar daukacin sojojin kasar Amurka daga kasar Iraki na daga cikin manyan abubuwa masu mahimmanci da suka ja hankali kuma wanda aka yi galaba kansu, da suka biyo bayan namijin kokari da kishin kasar da jama'ar kasar Iraki suka nuna, Sannan, karbar bakoncin taron kungiyar hadin kan larabawa da kasar ta Iraki ta yi ya kara nuna karfin gwamnatin kasar.
Ayatullah Ali Khamenei, ya kara da cewa, Wasu bangarori sun yi ta kokarin nuna cewa kasar Iraki, ba ta da wani matsayi a cikin kasashen larabawa, amma bayan taron kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ta gudana a Bagdada, kasar Iraki, a yanzu na kan gaba a cikin wannan kungiyar, kuma praministan kasar ke jagorantar ta.
A daya waje jagoran, ya bayyana cewa samun nasarori da ci gaban da kasar Iraki za ata yi don tabbatar da matsayinta tsakanin kasashe na iya fuskanatar wasu yan matsaloli, wanda ko dole ne kafin duk wata kasa ta samun yancin kanta da ci gaba da tabbatar da matsayinta tana bukatar shiri na gari da halin da zai sa ta cimma guri wanda mafi mahimmanci daga ciki sune ci gaban kimiya, da sake gina kasar hade da kayutata hanyoyin biya ma jama'ar kasar bukatocinsu, a game da hakan jagoran ya bada misali da kasar Iran, musamman a kan ci gaban kimiya da kasar ta samu da ma wasu sauren ci gaban da ma ba a taba tsamanin samunsu ba.
1088470


















captcha