IQNA

Daliban Jami'a A Kasar Afirka Ta Kudu Sun Bukaci A Yanke hulda Da Isra'ila

10:02 - September 05, 2012
Lambar Labari: 2405484
Bangaren kasa da kasa, dubban daliban jamia'a kasar Afirka ta kudu sun gudanar da wani gangami inda suka bukaci ahukuntan kasar da suka dauki matakan yanke duk wata hula musamman ta ilimi da al'adu da haramtacciyar kasar Isra'ila da ke shan jinin palastinawa fararen hula marassa kariya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa dubban daliban jamia'a kasar Afirka ta kudu sun gudanar da wani gangami inda suka bukaci ahukuntan kasar da suka dauki matakan yanke duk wata hula musamman ta ilimi da al'adu da haramtacciyar kasar Isra'ila da ke shan jinin palastinawa fararen hula marassa kariya tsawon shekaru.

Daliban jami'oin kasar Afrika ta kudu sun yi kira da a kawo karshen hulda ta al'adu da ilimi da h.k. Isra'ila. Daliban jami'ar Witwatersrand da ke kasar ta Afrika ta kudu sun fitar da wata sanarwa a jiya litinin inda su ka ce: "Bayan haramta sayen kayan da aka kera a Isra'ila da aka yi, kuma yana da kyau a kawo karshen hulda da ita ta fuskar al'adu da kuma ilimi." Bayanin daliban jami'ar ya ci gaba da cewa: "Al'ummar Afrika ta kudu tana bada cikakken goyon bayanta ga palasdinawa.

Saboda haka suna nuna cikakken goyon bayansu da dakatar da hulda ta al'adu da ilimi da Isra'ila." Tun a shekarar bara ne jami'ar Witwatersrand ta kawo karshen musayar fasaha tsakaninta da jami'ar Ben Gorion da ke Telaviv. Da dama daga cikin al'ummar kasar Afrika ta kudu suna daukar cewa h.k. Isra'ila tana hulda da palasdinawa daidai da yadda fararen fata su ka yi hulda da bakaken fatar kasar.

1091636














captcha