IQNA

Jami'an Qatar da Lebanon sun tattauna kan karfafa hadin gwiwar kur'ani

15:33 - October 16, 2025
Lambar Labari: 3494038
IQNA - Ministan awqaf da harkokin muslunci na kasar Qatar ya ziyarci gidan radiyon kur’ani na kasar Lebanon a wata ziyarar da ya kai birnin Beirut.

Ghanem bin Shaheen bin Ghanem Al Ghanim da jami'an gidan rediyon sun tattauna kan hanyoyin karfafa hadin gwiwar kur'ani a tsakanin kasashen biyu.

Maher Saqal jami'in gidan rediyon kur'ani mai tsarki na kasar Lebanon ya bayyana tarihin gidan rediyon da kuma makomarsa a nan gaba.

Ya kuma ambaci ci gaban ayyukan rediyo, da yin amfani da hanyoyin samar da makamashi na zamani, da gabatar da shirye-shirye na addini da na ilimantarwa daban-daban da kwasfan sauti da bidiyo akan wannan kafar sadarwa.

Ministan na Qatar ya mika wa Maher Saqal kwafin kur’ani mai tsarki.

Ya kuma ziyarci Asusun Zakka na Beirut, tare da rakiyar Sheikh Abdullatif Daryan, babban Mufti na kasar Lebanon.

Jakadan Qatar a Lebanon Saud bin Abdulrahman Al Thani da tawaga daga ofishin jakadancin Qatar ne suka halarci ziyarar.

A yayin wannan ziyarar, an gabatar da tawagar ta Qatar ga sassa daban-daban na asusun zakka na kasar Lebanon da shirye-shirye da ayyukanta daban-daban.

Mohamed Ibrahim Jozo, shugaban kwamitin amintattu na asusun, ya jaddada cewa, ya samu gagarumin ci gaba na kashi 44% a albarkatunsa a farkon rabin shekarar 2025, kuma ya fadada ayyukansa zuwa rassa 10 daga arewa zuwa kudancin kasar Lebanon.

Ya kara da cewa asusun zakka na kasar Labanon ya zama cibiyar kiyaye zaman lafiya ga iyalai, marayu, dalibai, marasa lafiya, da masu bukata ta musamman.

 

 

3495010

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kur’ani karfafa hadin gwiwa addini zakka
captcha