IQNA

23:18 - September 17, 2012
Lambar Labari: 2413784
Bnagaren kasa da kasa, babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar ya yi kida da a fitar da wasu dokoki na kasa da kasa da za su hana cin zarafin addinai da aka safkar daga sama tare da daukar tsauraran matakai na hukunci akan duk wanda ya yi haka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa sheikh Ahmad Tayyib babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar ya yi kida da a fitar da wasu dokoki na kasa da kasa da za su hana cin zarafin addinai da aka safkar daga sama tare da daukar tsauraran matakai na hukunci akan duk wanda ya yi hakan a cikin duniya.
an shirya kara da za agabatar a gaban shari’a kan wasu yahudawan sahyuniya masu wulakanta kur’ani mai tsarki a cikin yankunan palastinawa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye domin tabbatar musu da cewa musulmi ba za su amince da abin da uke yi ba na keta alfarma kur’ani da sauran ababe masu alfarma a cikin addinin muslunci.
A bangare guda kuma a ci gaba da mayar da martanin da malaman addinin muslunci gami da masana suke yi kan malamin gwamnatin Qatar Yusuf Kardawi, ministan mai kula da harkokin addinin muslunci a palastinu Muhmud Habbash ya bayyana cewa fatawar da Yusuf Kardawi ya bayar da ke hana sauran musulmi ziyartar masallacin Qods mai alfarma ta sabawa koyarwar alkur’ani mai tsarki da kuma sunanr manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
A kwanakin baya ne Yusuf Kardawi da ake kallonsa amtsayin daya daga cikin mamalan duniyar sunna, kuma daya daga cikin malaman da suka taka rawa a baya domin ganin sun wayar da kan muslulmi kan babbar barazanar da ke tattare da kulla alaka da musulmi suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, amma a halin yanzu ya zama malamin fadar sarkin Qatar, inda yake bayar da fatawowyi da suka yi daidai da abin da sarkin kasar ke bukatar ji, kasantuwarsa daya daga cikin karnukan farautar yahudawa.
1099184

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: