IQNA

Zanga-Zangar Musulmi Ta Tayarwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila Hankali

17:59 - September 19, 2012
Lambar Labari: 2415460
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci a birnin Qods ya bayyan acewa jerin gwanon da musulmi suka yi a fadin duniya domin nuna fushi kan cin zarafin manzo hakan ya tayar da hankalin haramtacciyar kasar Isra’ila matuka tare da saka yahudawa cikin firgita.
Kamfanin dillancin labbaran iqa ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI, cewa daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci a birnin Qods ya bayyan acewa jerin gwanon da musulmi suka yi a fadin duniya domin nuna fushi kan cin zarafin manzo hakan ya tayar da hankalin haramtacciyar kasar Isra’ila matuka tare da saka yahudawa cikin firgita da damuwa.
A wani labarin kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran Dakta Fereydoun Abbasi ya bayyana wani sabon makirci na dakatar da cibiyar nukiliyan kasar da ke Fordo da makiya suka yi jin kadan kafin bukatar da jami’an hukumar makashin nukiliyan ta duniya suka gabatar na ziyarar cibiyar.

Dakta Abbasi ya ce a ranar juma’ar da ta gabata wasu sun yi amfani da abubuwa masu fashewa wajen katse hanyar da ke kawo wuta ga wannan cibiyar, wanda hakan wata hanya ce ta lalata bututun tace sinadarin uranium da ke wajen. Dakta Abbasin ya kara da cewa kwatsam sai ga shi jami’an hukumar kula da makamashin nukiliyan ta duniya sun bukaci su kawo ziyara ta ba zata zuwa wannan cibiyar. Jami’in na Iran ya sanya shakku kan wannan lamarin yana mai cewa mai yiyuwa ne akwai alaka tsakanin katse wutar da kuma wannan ziyarar? Don haka shugaban hukumar nukiliyan ta Iran ya ja kunnen hukumar IAEA din dangane da batun kutsawar ‘yan ta’adda da masu kafar ungulu cikin hukumar.

A wata sabuwa kuma kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ramin Mehmanparast ya yi Allah wadai da kokarin da wasu kafafen watsa labarai suke yi na murguda maganganun manyan jami’an Iran don cimma wata manufa ta su yana mai musanta cewa Iran ta aike da sojojinta kasar Siriya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran yana mayar da martani ne ga kokarin da wasu kafafen watsa labarai suka yi na sauya maganar da babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi dangane da taimakon da Iran take ba wa gwamatin Siriya a fagen irin kwarewar da take da ita.

1101013












































captcha