To jigon shirin namu na yau shi ne yadda ake ci gaba da kashe musulmi a kasar Myanmar.
Da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji shirin kamar yadda zai gudana.
***
A cikin kwanakin baya bayan nan sunan kasar Myanmar, wacce a baya aka fi sani da Burma ya sake shiga bakin kafafen watsa labaru. Sai dai a wannan karon ba saboda bada lambar yabo ta kare hakkin bil'adama ga daya daga cikin 'yan siyasar kasar ba, sai dai saboda yi wa musulmi kisan kiyashi da ake yi. Mabiya addinin Buddha da kuma sojojin kasar ta Myanmar ne su ke yi wa musulmin kisan kiyashi. Hakan tana ci gaba da faruwa ba tare da fitacciyar 'yar siyasar kasar Asan su chi da ta sami kyautukan yabo daga turai ta buda baki ta yi tir da abinda ya ke faruwa ba a cikin wannan kasa. A lokacin ganawar da aka yi a tsakanin Un son Chi da kuma shugaban tarayyar turai a babban birnin kasar Nypyido, ta fadi cewa;
"Ba zan iya yin maganar da ta ke nuni da cewa ina bada kariya ga musulmin Rohinga ba."
Kamfanin Dillancin Labarun faransa da ya ke sharhi akan matsayar ta Un Son Chi, ya ce; "Zabar yin shiru akan abinda ya ke faruwa da musulmi da ta yi, ya jefa masu goya mata baya na kasa da kasa cikin damuwa."
Rahotanni da bayanan da aka tattara akan abinda ya faru da musulmin kasar a cikin shekaru 20 na bayan nan, sun tabbatar da cewa adadin wadanda aka yi wa kisan kiyashin sun kai 100, 000. An kone dukkanin kananan kauyuka da birane hudu da musulmin su ke rayuwa a cikinsu a yankin Rakhin.
Mayanmar kasa ce da ta ke a gabacin Asiya wacce kuma mafi yawancin mutanenta mabiya addinin Buddha ne. Gwamnatin kasar ba ta daukar musulmin da adadinsu ya kai dubu dari takwas a matsayin 'yan kasa ba , saboda haka ta ke son korarsu zuwa wata kasa. Shugaban kasar na yanzu Angusan Sochi yana da niyyar sake tsayawa takar aa shekarar 2016 saboda haka yana da bukatar kuri'un mabiya addinin na Buddha.
Shirun da 'yar siyasar kasar ta yi akan kisan musulmi ya jawo mata suka daga wani sashe na masu kare hakkin bil'adama. Ana Robertaz mai fafutukar kare hakkin bil'adam ta kasar Myanmar da ke kasar Birtaniya, ta bayyana takaicinta akan matsayar ta Un So Chi da cewa:
"Hakikanin gaskiya abin takaici ne cewa ta dauki wannan matsayin kuma mutane suna cikin fushi saboda ba ta zama mai gaskiya ba a tare da su."
Shi ma shugaban kungiyar kare hakkin bil'adama na Human Right Watch, Bard Adams ya ce; " Ta yi watsi da dama mai yawa da ta samu domin bayyana matsayarta akan wannan lamarin. Da akwai abinda za ta iya yi wanda ba ta y ba."
Wani jami'an na kungiyar kare hakkin bil'adama na "Equality Right" da ke birtaniya Amal Do Chekra ta ce:
"Kina da labari akan duk abinda ya ke faruwa, saboda haka abin takaici ne saboda yadda kika za bi yin shiru wanda zai iya haifar da matsala mai girma."
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kisan kiyashin da ake yi wa musulmin kasar ta Myanmar a matsayin cuta mafi girma da ake yi wa tsiraru a duniya. Kuma har ya zuwa yanzu shugaban kasar bai ce wani abu ba akansa.
Al'ummar Rohinga na waje suna rayuwa ne a cikin kasashen Bagaladesh da Pakistan da Saudiyya da Thailand da Malasiya da Idonesia da wasu kasashen turai da kuma Austiralia. Asalinsu jikokin 'yan kasauwa da masu yawan bude ido larabawa ne da su ke da al'adu da harshe nasu na kansu. Bayan da kasar Myanmar ta sami 'yanci daga mulkin mallakar Birtaniya a 1948 an rika daukar al'ummar Rohinga a matsayin tsararu a cikin wannan kasa. Kuma tun daga lokacin da sojoji su ka kwace mulki a 1962, sun dauki wani salon siyasa wacce ta haifar da yi wa musulmi kisan kiyashi musamman ma dai a yammacin kasar.
Kaso 89% na mutanen Myanmar mabiya addini Buddha ne yayin da adadin musulmi bai uwce kaso 4%. Wato a tsakanin mutane miliyan 55 da ake da su, musulmi su ne dubud dari takwas.
Jaridun gwamnatin Myanmar suna baiwa musulmin kasar sunanye na wulakanci da cin fuska. Suna kiransu da sunan bakaken mutane ko larabawa ko kuma 'yan kasar Bangaladesh. Kuma wariyar da ke nuna musu ya maida su zama wadanda ba su da kasa. A kowace shekara wajibi ne kodanne iyali na musulmi su dauki hoto cikin jam'i su mikawa gwamnati. Idan aka ga sabuwar haihuwa a cikinsu, ko kuma wani daga cikinsu ya mutu, to za su biya gwamnati haraji.
Haka nan kuma gwamnatin kasar ta yi wa musulmin iyakoki masu yawa. An hana mu hakkin mallakar kasa haka nan kuma basu da hakkin yin karatu, kuma basu da hakkin cin mariyar hidima daga gwamnati. Kuma gwamnati da mabiya addinin Buddha suna tilasta musu yin hijira zuwa waje. A cikin gida ba su da hakkin yin tafiya daga wani gari zuwa wani gari, idan kuwa har za su yi to sai sun biya gwamnati haraji. Idan kuwa musulmi yana son kafa wani shagon kasuwanci to wajibi ne a gare shi ya yi tarayya da mabiya addinin Buddha. Musulmi ne ya ke da hannun jari shi kuwa dan Buddha ba shi da komai a ciki, amma kuma duk ribar da aka samu sai ya sami nashi kason.
Rikicin bayan na ya samo asali bisa abinda mabiya addinin Buddha su ka riya cewa; musulmin sun kashe wace mace daga cikinsu. Saboda haka su ka kona gidajen musulmi tare da tilastawa dubbai daga cikinsu yin hira zuwa Bangaladesh. Sai dai ita ma kasar ta Bangaladesh din ta rufe iyokinta ta hana musulmin shiga cikinta. Saboda haka sun yada zango akan iyakar kasarsu da kuma Bangaladesh a cikin mummunan yanayi da hali.
Kasashen yammacin turai masu bugun kirji da kare hakkin bil'ada sun yi guma da bakunansu ba tare da dauki wani mataki ba. Da kuwa a ce kasar ta mayanmar tana a wani bagire ne mai amfani ga turai to da ba za su yi shiru ba, da sun san matakin da ya kamata su dauka.
Mafi muni shi ne matsayin da Un so Chi ta dauka na yin shiru akan kisan da ake yi wa 'yan kasarta saboda kawai su musulmi ne.