IQNA

Mahukumtan Iran Sun Maraba Da Bayani Kan Bawa Palasdinu Matsayi A MDD

12:50 - December 02, 2012
Lambar Labari: 2457077
Wakilin kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar amincewa da daga matsayin Palasdinu a Majalisar Dinkin Duniya zuwa matakin mai sanya ido a Majalisar lamari da ke fayyace cewa lalle duniya tana kara fahimtar zaluntar al'ummar Palasdinu da ake yi.
Kamfanin dillancin labarai Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa;A zantawar da ya yi da kamfanin dillancin labaran kasar Iran na IRNA a jiya Juma'a dangane da kuri'ar da kasashen duniya suka kada a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na amincewa da daftarin neman amincewa da Palasdinu a matsayin mai sanya ido a Majalisar; Muhammad Khazza'i ya bayyana cewar wannan wani babban lamari ne da ke fayyace cewar duniya tana kara fahimtar irin bakin zaluncin da al'ummar Palasdinu ke fuskanta.
Khazza'i ya kara da cewar duk da cewa amincewa da Palasdinu a matsayin mai sanya ido a Majalisar Dinkin Duniya baya nufin kasancewarta cikekkiyar mamba a Majalisar, amma hakan yana kara fayyace samun goyon baya ne ga al'ummar Palasdinu a matsayin siyasar kasa da kasa.
A ranar Alhamis da ta gabata ce kasashe 138 na duniya suka kada kuri'ar amincewa da daftarin kudurin neman kara daga matsayin Palasdinu a Majalisar Dinkin Duniya a matsayin mai sanya ido a Majalisar, yayin da wasu kasashe musamman Amurka, Canada, H.K.Isra'ila da sauransu suka kada kuri'ar kin amincewa da daftarin kudurin, wasu kasashe 41 na daban kuma ciki har da Birtaniya suka ki bayyana matsayinsu ta hanyar kin kada kuri'ar.

1145679
captcha