IQNA

Jagora Ya Gana Da Mahalarta Taron Malaman Jami'oin Kasashen Musulunci Da Farkawa Ta Musulunci

11:19 - December 12, 2012
Lambar Labari: 2462583
safiyar yau Talata (11-12-2012) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da daruruwan malaman jami'a da sauran masana mahalarta taron kasa da kasa na "Malaman jami'oin kasashen musulmi da farkawa ta Musulunci" da aka gudanar.
A safiyar yau Talata (11-12-2012) ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da daruruwan malaman jami'a da sauran masana mahalarta taron kasa da kasa na "Malaman jami'oin kasashen musulmi da farkawa ta Musulunci" da aka gudanar. A lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a wajen taron, Jagoran ya yi karin haske dangane da matsayin Musulunci da shari'ar Musulunci haka nan kuma da yanayin mutane a kasashen da aka yi juyin juya hali (a baya-bayan nan) da kuma irin kalubale da hatsarin da ke a gabansu.

Yayin da ya ke ishara da irin rawar da fitattun cikin al'umma za su taka wajen samar musu da sa'ada da kuma ‘yantar da su daga cikin matsalolin da suke fuskanta, Jagoran cewa ya yi: Bisa wannan mahangar ana iya cewa wannan taro na "Malaman jami'oin kasashen musulmi da farkawa ta Musulunci" yana da wani muhimmanci na musamman.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana ikhlasi, jaruntaka, nuna sanin ya kamata, aiki da kokari a matsayin sharudda na asali na samun nasarar irin rawar da malaman jami'an da sauran masana cikin al'ummar za su taka wajen samar musu da rayuwa mai kyau. Daga nan sai ya ce: Farkawa ta Musulunci da tabbatuwar hakan cikin al'ummar musulmi, wani lamari ne mai girman gaske da a halin yanzu duniya take ganinsa sannan a wasu kasashen kuma ya yi sanadiyyar bullar juyin juya hali da sauya lalatattun gwamnatocin da suke wadannan kasashen.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin damuwa da tsoron da makiya suke ciki sakamakon wannan lamari na 'farkawa ta Musulunci', Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Wadannan mutane suna ta kokari ba dare ba rana wajen ganin ba a yi amfani da Kalmar ‘farkawa ta Musulunci' wajen bayyana irin wannan gagarumin yunkuri da ke faruwa a wanann yankin ba, don kuwa makiya suna cikin tsananin damuwa sakamakon bayyanar Musulunci na hakika.

Jagoran ya ci gaba da cewa: wadannan mutanen ba sa tsoron Musuluncin da ya damu da cika aljihunsa, Musuluncin da ba abin da ya damu da shi in banda almubazzaranci da fasadi da kuma Musuluncin da ba shi da wani matsayi a idon al'umma, to amma hantarsu tana kadawa a duk lokacin da suka ga Musuluncin aiki da daukar matsaya, Musulunci irin na al'umma, Musuluncin da ya dogara da Allah da kuma Musuluncin da ya yi amanna da kuma yarda da alkawarin Ubangiji.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Mu mun yi imani da cewa wannan gagarumin yunkurin (da ke faruwa a halin yanzu) wata farkawa ce ta hakika ta Musulunci sannan kuma yana ci gaba da yaduwa ta yadda ba cikin sauki za a iya karkatar da shi ba.

Haka nan kuma a ci gaba da bayanin dalilin da ya sanya ake kiran wannan farkawa da al'umma suka samu da sunan farkawa ta Musulunci, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Irin take na Musulunci da mutane masu juyin juya halin yankin nan suke rerawa da kuma irin rawar da masu riko da Musulunci suka taka wajen shirya irin tarurrukan da suka yi sanadiyyar kifar da lalatattun gwamnatocin yankin nan, dukkaninsu abubuwa ne da suke tabbatar da cewa wannan yunkuri wani yunkuri ne na Musulunci.

Jagoran ya bayyana irin kuri'ar da al'ummomin kasashen da aka yi wadannan juyin suka kada wa jam'iyyu da kungiyoyi masu kishin Musulunci a matsayin wani dalilin da ke tabbatar da cewa wannan yunkuri na al'umma wani yunkuri ne na Musulunci. Daga nan kuma sai ya ce: A yau ma idan har aka gudanar da zabe na hakika a mafi yawa daga cikin kasashen musulmi, sannan kuma jagorori da ‘yan siyasa masu kishin Musulunci suka shigo fage, to kuwa mutane za su kada wa masu kishin musulunci kuri'a ne.

A ci gaba da jawabin nasa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tunatar da mahalarta taron wasu batutuwa masu muhimmanci.

Sanin ya kamata da kuma abubuwa masu cutar da wannan yunkuri musamman a kasashen Masar, Tunusiya da Libiya shi ne lamari na farko da Ayatullah Khamenei yayi ishara da shi a wannan bangaren, daga nan sai ya ce: baya ga fahimtar abubuwa masu cutarwar, wajibi ne a ci gaba da bin diddigin manufofin wadannan yunkuri da kuma juyin. Don kuwa matukar dai ba ayyana manufofin da ake son cimmawa ba, to gwuiwoyin mutane za su yi sanyi.

Jagoran ya bayyana ‘yantuwa daga sharri da ikon ‘yan mulkin mallaka na duniya a matsayin daya daga cikin manufofin wannan farkawa ta Musulunci daga nan sai ya ce: Wajibi ne a bayyanar da wannan batu a fili, don kuwa duk wani tunanin cewa girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka mai yiyuwa ne su amince da kuma tafiya tare da wadannan yunkuri na Musulunci, kuskure ne.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: A duk inda Musulunci da kuma kishin Musulunci yake, to kuwa Amurka za ta yi kokari da dukkan karfinta wajen kawar da su, duk kuwa da cewa a fili za ta dinga sakin fuska da nuna cewa tana tare da su.

Haka nan kuma yayin da ya ke bayyana cewar wajibi ne juyin juya halin yankin nan su shata da kuma bambance kan iyakokinsu da ma'abota girman kan duniya, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Mu dai ba wai muna cewa ne su sanar da yaki a kan ma'abota girman kan ba ne, to amma matukar dai ba su shata kan iyakokinsu ba, to kuwa za su fada tarkon yaudara.

Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da irin yadda ma'abota girman kan suke amfani da karfi na kudi, makami da ilimi wajen tabbatar da ikonsu a kan duniya, Jagoran cewa ya yi: Duk kuwa da irin wannan karfin da suke da shi, to amma daya daga cikin manyan matsalolin da kasashen yammaci suke ciki a halin yanzu shi ne rashin wani sabon tunani da koyarwa da za su gabatar da shi ga bil'adama, alhali kuwa kasashen musulmi suna da sabbin tunani da kuma taswirar hanya.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar addinin Musulunci dai yana da sabuwar taswirar hanyar da kuma tunani ga bil'adama inda ya ce: Hakan wani bangare ne na irin karfin da duniyar musulmi take da shi ta yadda idan har aka tsara manufofi suka yi daidai da hakan, to kuwa makami, dukiya da kuma ilimin kasashen yammaci ba za su yi wani tasiri ba.

Ayatullah Khamenei ya bayyana tabbatar da koyarwar Musulunci da shari'arsa a matsayin wata manufar ta daban mai muhimmanci ta wannan yunkuri na musulunci inda yace: A halin yanzu dai ana nan ana ta kokari ba kama hannun yaro wajen nuna cewa shari'ar Musulunci ba za ta iya tafiya tare da irin ci gaba na duniya ba, alhali kuwa Musulunci addini ne da zai iya biyan dukkanin bukatun bil'adama na dukkanin karnoni da kuma dukkanin ci gaban da dan'adam ya samu.

Jagoran juyin juya halin ya nuna tsananin damuwa da bakin cikinsa dangane da wasu jama'a da kungiyoyi wadanda suke jingina kansu da Musulunci wadanda kuma sakamakon irin ayyuka na koma baya da suke yi ake bayyana musulunci a matsayin wani addini na koma baya wanda babu ruwansa da duk wani ci gaba da na duniya.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana tabbatar da tsari a matsayin wata manufar ta daban ta wannan farkawa ta Musulunci, sannan kuma yayin da yake ishara da wasu yunkure-yunkure da suka faru cikin tarihin yankin kasashen arewacin Afirka wadanda kuma suka sha kashi sakamakon rashin tsarin da suka fuskanta, Jagoran ya bayyana cewar: Matukar dai ba a tsara lamurra yadda ya kamata ba a kasashen da suka yi juyi, sannan kuma ba a tabbatar da karfafaffen tushe ga wannan juyin ba, to kuwa za a fuskanci matsala da hatsari.

Jagoran juyin juya halin ya bayyana kiyaye goyon bayan al'umma a matsayin daya daga cikin lamurra masu muhimmanci na wadannan juyin inda ya ce: Karfi na hakika dai yana hannun mutane ne. A duk irin mutane suka kasance tare da jami'an gwamnatinsu da kuma ba su kariya, to kuwa Amurka da ma wadanda suke gaban Amurka, babu wani abin da za su iya.

Wani lamarin kuma da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da shi batun karfafa matasa a bangaren ilimi da kuma samar da ci gaba na ilimi da fasaha inda ya yi ishara da da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin misalin da ke tabbatar da muhimmancin hakan. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Kasar Iran, kafin nasarar juyin juya halin Musulunci, ta kasance ne a matsayin na kurya a fagen ilimi. To amma a halin yanzu albarkacin Musulunci da kuma juyin juya halin Musulunci tana a matsayi na sama-sama ne a duniya. Wannan kuwa wani lamari ne da cibiyoyin kididdiga na kasa da kasa suke tabbatar da shi.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Tsarin Musulunci na Iran ya tabbatar da cewa ana iya kai wa ga matsayi na koli na ilimi ta hanyar riko da kuma dogaro da Musulunci da kuma shari'ar Musulunci.

Wani batun kuma da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da shi a yayin wannan ganawar shi ne batun hadin kan musulmi da kuma muhimmancin hakan bugu da kari kan bukatar da duniyar musulmi take da shi ga wannan batu inda ya ce: Amurka da kasashen yammaci suna ta kokari ta hanyar amfani da batun ‘shia da sunna' ‘kabilanci da ‘yan kasanci' wajen haifar da sabani da rarrabuwan kai tsakanin musulmi. A saboda haka wajibi ne dukkanin al'umma su yi taka tsantsan sannan kuma su kalli lamurra da wannan mahangar.

Har ila yau kuma yayin da ya ke bayanin cewa duk da irin kokari da kuma makirce-makircen da ma'abota girman kai suke yi amma duniyar musulmi tana ci gaba. Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Daya daga cikin alamun irin wannan ci gaban, shi ne yakin kwanaki takwas da ya gudana tsakanin wasu al'ummar Palastinu da suke zaune a wani dan karamin waje mai suna Gaza da kuma gwamnatin sahyoniyawa wacce take ikirarin mallakar sojojin da suke karfi a yankin nan ta yadda daga karshe dai sharuddan da Palastinawa suka kafa ne aka yi aiki da shi wajen tsagaita wuta.

Jagoran ya kara da cewa: Shin shekaru goman da suka gabata, wani zai iya gaskata cewa hakan za ta faru?

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Lalle muna jinjinawa Palastinawa, muna jinjinawa Hamas da Jihadi Islami da kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa a Gaza, wadanda suka nuna irin wannan jaruntaka.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A bangare na irin isar da godiya ta ga dukkanin ‘yan gwagwarmayar Palastinawa albarkacin wannan sadaukarwa da kokari da kuma hakurin da suka nuna.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana yakin kwanaki takwas na Gazan a matsayin wani darasi mai muhimmanci ga al'ummar Palastinu da kuma dukkanin musulman duniya inda ya ce: Yakin Gaza ya tabbatar da cewa matukar dai dukkanin al'umma suka hada kansu waje guda, sannan kuma suka yi hakuri da dukkanin whalhalu, to kuwa alkawarin Allah na samar da mafita da kuma sauki bayan wahala zai tabbata.

Wani lamari kuma da Jagoran ya yi ishara da shi, shi ne batun kasar Bahrain wanda ya ce abin bakin ciki ne yadda duniyar musulmi ta yi gum da bakinta dangane da abin da ke faruwa a kasar Bahrain din wanda yace ya samo asali ne saboda irin kallo na kuskure da ake yi wa lamarin.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan abin da ke faruwa a kasar Siriya da kuma mahangar Iran kan hakan, Jagoran cewa ya yi: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai tana adawa da zubar da jinin kowani musulmi, to amma wadanda suke da laifi cikin yanayin da kasar Siriya take ciki a halin yanzu su ne mutanen da suka haifar da yakin basasa da kashe ‘yan'uwa a kasar Siriyan.

Daga karshe dai Jagoran ya bayyana cewar wajibi ne a magance dukkanin matsaloli da kuma bukatun al'ummomi ta hanyar ruwan sanyi ba tare da zubar da jini ba.

Kafin jawabin Jagoran dai sai da wasu mutane 7 daga cikin masana da malaman jami'oin kasashen musulmin suka gabatar da jawabansu da kuma bayyanar da mahangarsu kan irin sauyin da ke faruwa a yankin nan da kuma irin farkawar da al'umma suka yi.

Jawaban nasu kuwa ya kumshi batutuwa da suka hada da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran karkashin jagorancin marigayi Imam Khumaini (r.a) ita ce mafarin wannan farkawar, kamar yadda kuma suka tabbatar da wajibcin hadin kai tsakanin al'ummar musulmi wajen magance makirce-makircen makiya. Haka nan kuma sun bayyana wajibcin amfani da irin kwarewar da aka samu ta hanyar nasarorin da kungiyoyin gwagwarmaya suka samu wajen ciyar da manufofin al'umma gaba. Kamar yadda kuma suka yi kira da a shata kan iyaka da kuma bayyanar da mahanga a fili dangane da girman kan duniya da kuma haramtacciyar kasar Isra'ila a kasashen da suka yi juyi. Har ila yau kuma jawabin nasu ya kumshi yin Allah wadai da irin halin ko in kula da cibiyoyin kasa da kasa da kuma kasashen musulmi suka yi dangane da irin kisan gillan da ake yi wa al'ummar Bahrain.
1152054
captcha