IQNA

An Bayyana Ranar Bayar Da Kyautuka kan Karatun Kur'ani A kasar Sudan

23:26 - January 15, 2013
Lambar Labari: 2480950
Bangaren kasa da kasa, an bayyana ranar 13 ga wata Janairu a matsayin ranar bayar da kyautuka kan karatu da kuma harder kur'ani mai tsarki a kasar Sudan domin hakan ya zama wata rana ta girmama ayyukan da suka shafi kur'ani mai tsarki a matsayi na kasa baki daya kamar dai yadda majiyoyin ma'akkatar kula da harkokin kur'ani ta kasar ta sanar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mod.gov.sd cewa, a yau an bayyana ranar 13 ga wata Janairu a matsayin ranar bayar da kyautuka kan karatu da kuma harder kur'ani mai tsarki a kasar Sudan domin hakan ya zama wata rana ta girmama ayyukan da suka shafi kur'ani mai tsarki a matsayi na kasa baki daya kamar dai yadda majiyoyin ma'akkatar kula da harkokin kur'ani ta kasar ta sanar a yau.

A wani labarin kuma Shugaban kasar Sudan Umar Hasan al-Bashir ya bayyana cewar ko da wasa gwamnatinsa ba za ta yi watsi da koyarwar Musulunci ba, sannan kuma za a tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar ne bisa koyarwar Musuluncin.
Shugaban na Sudan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi a wajen rufe gasar karatun Alkur'ani mai girma da aka gudanar a daren jiya a birnin Khartoum babban birnin kasar, inda ya ce gwamnatinsa dai ba za ta taba yin watsi da koyarwar Musulunci da ta rika ba.
Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan masu adawa da siyasar da gwamnatin take gudanarwa wadanda kuma suka hada baki da 'yan tawayen kasar da kuma sanya hannu kan wata yarjejeniya a tsakaninsu, shugaban Al-Bashir ya bayyana su a matsayin ha'inai inda ya ce babu yadda za a raba gwamnati da addini a yayin rubuta sabon kundin tsarin mulkin, duk kuwa da cewa 'yan adawan ba sa son ganin an yi aiki da koyarwar Alkur'ani mai girma da kuma sanya su cikin kundin tsarin mulkin.
Shugaban ya bayyana cewar komawa ga koyarwar Musulunci ita ce kawai hanya guda ta magance dukkanin matsalolin da al'ummomi suke fuskanta.

1171457


captcha