IQNA

Jami’ar Azhar Ta Ce Za Ta Kara Fadada Aalakarta Da Fadar Vatican Ta Mabiya Addinin Kirista

19:57 - February 14, 2013
Lambar Labari: 2496506
Bangaren kasa da kasa, babbar jami’ar musulunci ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ta ce za ta fadada alaka da fadar Vatican ta mbaiya addinin kirista daga bangaren darikar katolika domin kara samun daidaito tsakanin bangarorin biyu saboda samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ahram, cewa babbar jami’ar musulunci ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ta ce za ta fadada alaka da fadar Vatican ta mbaiya addinin kirista daga bangaren darikar katolika domin kara samun daidaito tsakanin bangarorin biyu saboda samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu kamar dai yadda shugaban jami’ar ya fada.
A bangare guda kuma shugaban mabiya darikar katolika Paparoma Benedict na 16 ya bayyana cewar lalle ya fuskanci mawuyacin yanayi cikin 'yan shekarun nan lamarin da ya sanya shi tunanin sauka daga wannan matsayi nasa.
Paparoma Benedict ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi a gaban dubun dubatan mutanen da suka taru a fadar tasa ta Vatican a jiya laraba, karon farko da ya fara fitowa bainar jama'a tun bayan da ya sanar da aniyarsa ta yin murabus din, inda ya gode wa jam'ar dangane da abin da ya kira goyon baya da kuma addu'oin da suka dinga yi masa.
Paparoman ya ce ya dau wannan matsaya ta yin murabus din ne don amfani cocin katolika bayan addu'oi na tsawon lokaci duk kuwa da hatsari da ke cikin hakan.
A ranar litinin din da ta gabata ce Paparoma Benedict din ya sanar da cewa zai yi murabus a ranar 28 ga watan Fabrairun nan da muke ciki. Shi ne dai Paparoma na farko cikin shekaru dari shida da suka gabata da ya yi murabus daga wannan matsayin.
1188176


captcha