IQNA

Imam Khamenei: Al'ummar Iran Za Su Ba Maras Da Kunya A Lokacin Zabe Mai Zuwa

9:09 - May 29, 2013
Lambar Labari: 2540446
Bangaren siyasa, a taron bukukuwan zagayowar shekarar da aka ‘yanto garin Khoramshahr daga hannun sojojin mamayan Iraki da ake gudanarwa a jamhuriyyar musl;unci ta Iran, a safiyar Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarcin bikin yaye daliban jami'ar dakarun kare juyin juya hali ta Imam Husain (a.s) da ke birnin Tehran.


Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagora cewa, Jim kadan bayan isowarsa, Jagoran ya kai ziyarar ban girma zuwa ga makabartar shahidai da ke cikin Jami'ar inda ya karanta musu Fatiha don nema musu karin matsayi a wajen Allah kamar yadda kuma ya halarci wani faretin ban girma da dakarun suka yi masa bugu da kari kan girmama wasu sojoji da suka sami raunuka a wajen yaki.
A lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa a wajen bikin, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana fitowar al'ummar Iran kwansu da kwarkwatarsu a lokacin zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 14 ga watan Yunin nan a matsayin wata bishara ga irin nasarori da ci gaban da juyin Musulunci da kuma gwamnatin Musulunci suka samu, sannan kuma yayin da yake kiran al'umma da su sanya ido sosai kan abubuwan da ‘yan takaran shugabancin kasar suke fadi don su gano da kuma zaban mutumin da ya fi dacewa. Kamar yadda kuma ya kirayi ‘yan takaran da su ba da himma wajen kiyaye koyarwar tsarin Musulunci da kuma nesantar kokarin bata sunan junansu da munanan halaye a lokacin yakin neman zabe inda ya ce: Cikin yardar Allah, makomar kasar nan da kuma wannan al'ummar al'ummar za ta kasance makoma ce mai kyau wacce za ta zamanto abin koyi ga sauran al'ummomi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Mu dai ba mu san wane ne zai zamanto shugaban kasa ba, ba mu san wane ne Allah zai juyar da zukatan mutane zuwa gare shi ba, to amma mun san cewa fitowar mutane yayin zaben wanda ke nuni da irin riko da mutane suke yi wa wannan tsarin ne, ko shakka babu hakan zai share fagen daukaka da kuma kare mutumcin wannan kasa ne a fage na kasa da kasa, sannan kuma zai zamanto abu mai faranta rai ga masoya da kuma bakanta ran makiya.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin farfagandar da makiyan al'ummar Iran suke yadawa da nufin kashe gwiwar mutane daga fitowa zaben, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Dalilin irin wannan farfagandar shi ne cewa idan har mutane suka shigo cikin fage da kuma fitowa kwansu da kwarkwatansu, to kuwa kashin makiyan ya bushe.
Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan maganganun da jami'an Amurka suke ci gaba da yi kan zaben na Iran, Jagoran cewa ya yi: Wasu mutane suna ta magana kan wannan zabe na Iran, alhali kuwa abin da suke yi a gidan yarin Guantanamo da kuma irin danyen aikin da jiragensu marasa matuka suke yi a kasashen Pakistan da Afghanistan, da wutar yakin da suke rurawa a yankin nan bugu da kari kan goyon baya ido rufe da suke ba wa azzalumar gwamnatin sahyoniyawa sun sanya su sun zamanto abin kyama a idanuwan mutane.
Haka nan kuma Jagoran ya bayyana cewar abubuwan da suke fadi dangane da zaben Iran wani lamari ne da ba shi da wani matsayin da jami'an gwamnati da al'ummar Iran za su mayar musu da martani. Daga nan sai ya ce: Tabbas irin wadannan maganganu za su kara wa al'ummarmu karfin gwuiwa ne, don kuwa hakan yana nuni da irin gagarumin matsayi da muhimmancin daga zaben Iran yake da shi a wajensu.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Shekaru 34 kenan masu kiyayya da al'ummar Iran suke kokarin tada fitina a kasar nan a duk lokacin zabe, alhali kuwa tsawon wannan lokacin sun sha kashi, sannan kuma cikin yardar Allah a wannan karon ma al'ummar Iran za su bada musu kasa a idanuwansu.
A saboda haka ne Jagoran ya kirayi al'umma da su sanya ido sosai wajen zaban dan takaran da ya dace inda ya ce: Wajibi ne mutane su fifita mutumin da zai share fagen daukaka da ci gaban wannan juyi da kuma wannan kasa, sannan kuma yake da karfin magance matsalolin da ake fuskanta da kuma tsayin daka a gaban makiya da kuma mai da Jamhuriyar Musulunci ta zamanto wani abin koyi a idanuwan raunana na duniya.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Bai kamata sabanin da ake samu tsakanin mutane wajen gano dan takaran da ya dace da kuma goyon bayan da kowa yake ba wa dan takaransa ya zamanto abin da zai haifar da rikici da fada a tsakanin mutane ba.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar doka ta tanadi yadda za a zabi shugaban kasa wanda shi jami'i mafi girma a bangaren gudanarwa a kasar nan, sannan kuma bisa wannan dokar ce za a yi aiki. A saboda haka bai kamata sabanin ra'ayi ya haifar da kace-nace ba.
Yayin da ya koma kan ‘yan takaran zaben shugabancin na Iran kuwa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wasu nasihohi ga ‘yan takaran da cewa: Wajibi ne ‘yan takara su kiyaye irin wannan fitowa da kumaji na al'umma, to amma su guji haifar da rikici.
Nasiha ta gaba da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi wa ‘yan takaran ita ce dangane da kudaden da za su kashe yayin yakin neman zabe ne inda ya ce: Mutane za su yi hukumci wa irin yadda ‘yan takaran suke gudanar da yakin neman zabensu da kuma irin kudaden da suke kashewa bugu da kari kan dabi'unsu. Ko shakka babu duk wani wanda ya yi kokarin diban kudaden Baitul mali da kuma wasu hanyoyi na haramun, to kuwa mutane ba za su yarda da shi ba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Abin da ke da muhimmanci cikin yakin neman zaben ‘yan takaran, shi ne tabbatar da irin shirin da ake da shi na tabbatar da matsayi da daukaka ta kasar nan da kuma wannan tsari na Musulunci.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Bai kamata a yayin yakin neman zabe a karfafa wa wasu masu bakar aniya na ciki da wajen kasar nan gwiwa ba, don kuwa makiya suna nan suna ta kai gwauro su kai mari wajen kashe wa mutane gwiwa. Abin bakin cikin shi ne cewa wasu daga cikin bakuna da alkalumma na wasu marasa tsoron Allah a cikin gida suna ci gaba da nanata abubuwan da makiyan suke fadi.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma babban kwamandan dakarun kasar Iran ya bayyana ba da kariya ga juyin juya halin Musulunci a matsayin daya daga cikin siffofin da wannan jami'ar ta Imam Husain (a.s) ta kebanta da ita inda ya ce: Daya daga cikin abubuwan da suka wajaba a tabbatar da su a fagen ba da kariya ga wannan juyin shi ne ingantacciyar fahimta koyarwa da kuma tunani na wannan juyin na Musulunci da kuma ci gaba da riko da hakan.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Tsawon wannan juyi na Musulunci, an sami wasu mutane da suka shigo fage ba tare da cikakkiyar masaniyar koyarwar juyin ba, don haka daga lokacin da suka fuskanci wata matsala, nan take su kan sauya da kuma kaucewa daga tafarkin juyin.
Kafin jawabin Jagoran sai da babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari da kuma shugaban jami'ar Imam Husain (a.s) ta dakarun kare juyin Admiral Murtadha Safari suka gabatar da jawabinsu da kuma ishara da irin ayyukan da dakarun kare juyin suka yi kuma suke ci gaba da yi, bugu da kari kan wadanda aka gudanar a jami'ar.
1234700




captcha