IQNA

18:05 - July 27, 2013
Lambar Labari: 2567642
Bangaren kasa da kasa, yan ta'addan Syria da ke samun goyon bayan yahudawa da wahabiyawa sun kona alkur'ani mai tsarki a ci gaba da kaddamar da harin da suke yi kan fararen hula da wuraren ibada a cikin wasu yankuna na kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yan ta'addan Syria da ke samun goyon bayan yahudawa da wahabiyawa sun kona alkur'ani mai tsarki a ci gaba da kaddamar da harin da suke yi kan fararen hula da wuraren ibada a cikin wasu yankuna na kasar musamman da suke iko da su.

Wani rahoton kuma yana cewa yan ta’addar kasar Siriya na kisan kan mai uwa da wabi a yankin home na halab. Gidan talbijin na Press TV wanda yake watsa shirye-shiryensa daga nan birnin Tehran ya habarta cewa ‘yan ta’addar kasar Siriya sun kashe fararen hula fiye da 50 tare da wani adadi na Sojojin Siriya wadandan ‘yan ta’adda suka kama a Hanin Asal dake kewayen Halab a jiya juma’a. ‘yan ta’addar sun kashe fararen hular ne tare da Sojojin ta hanyar harbinsu da bindiga.

Hanul Asal na daga cikin yankunan da Gwamnatin Siriya ke zarkin ‘yan ta’adda da amfani da makamai masu guba inda Gwamnatin tace ‘yan ta’adda suna amfani da makamai masu guba a kan fararen hula a wannan yanki na Hanul Asal.

Sojojin Syria sun sanar da samun nasarar kame daya daga cikin manyan jagororin kungiyar Nusra Front reshen kungiyar Alqaeda a yankin Sham da ake kira 'yan tawayen Syria. Kamfanin dilalncin labaran SANA ya nakalto daga rundunar sojin kasar ta Syria cewa, an kame jigon na kungiyar alqaeda ne a kusa da hubbaren Sayyidah Zainab (AS) da ke kusa da birnin Damscus, an kuma kashe wasu mayaka 49 dukkaninsu 'yan kasashen ketare da suke tare da shi. Wasu rahotannin kuma sun tabbatar da cewa sojojin na Syria sun kwace iko da garin Baniyas da ke cikin gundumar Tartus, bayan fatattakar 'yan ta'adda daga garin tare da kashe wani adadi mai yawa daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka mika kansu da makaman da ke hannunsu.

1264113Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: