Bangaren kasa da kasa, a wata ganawa da ta guadana a tsakanin bababn sakatare janar na kungiyar kasashen larabawa da kuma shugaban bababar cibiyar musulunci ta Azahar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo na Al-ahram cewa Shugaban Jami'ar Al-Azhar ta kasar Masar da kuma Babban sakataren.
kungiyar kasashen Larabawa sun jaddada wajibcin yaki da akidun wuce gona da iri wadanda suke bata fuskar addinin musulunci a kasashen larabwa.
Kamfanin dillancin labarai na Alqur'ani ya nakalto Sheikh Ahmad Tayyeeb shugaban Jami'an Al-Azhar da kuma Nabil Arabi Babban sakataren kungiyar kasashen larbawa wadanda suka gana a taron ministocin harkokin waje na kasashen larabawa wanda ake gudanar a birnin Alkahira suna fadar haka.
Sheikh Tayyeeb ya ce Jami'ar Al-Azhar zata yi yaki da wadannan mummunan ikidu ta hanyar yada akidun musulunci na gaskiya da kuma bude fagen muhawara da jawabai don kushe dukkan akidu masu munana fuskar addinin musulunci a kasashen larabawa.
A nashi bangaren Nabil Al-Arabi ya jaddada muhimmancin Jami'ar Al-Azhar a matsayinta na cibiyar ta yada addinin musulunci, wajen yakar yan ta'adda da kuma mummunan akidun da wasu ke dangantasu da addinin musuluni.
2612252