Kmafanin dilancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-sharq ta kasar Saudiyya cewa, a cikin wani bayani da ta fitar majalisar dinkin duniya ta bukaci haramtacciyar kasar Isra’ila da ta dakatar da wuce goda da irin da take yi na rusa gidajen palastinawa a yankuna gabacin quds da sauran yankuna.
Su ma a nasu bangaren Masu rajin kare hakin bil-adama na Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci da a dakatar da rusa gidajen Palastinawa cikin gaggawa. A wani rahoto da hukumar kare hakin bil-adama ta majalisar dinkin duniya ta fiyar a yau ta siffanta rusa gidajen na Palastinawa da Gwamnatin haramcecciyar kasar Isra'ila ke yi a matsayin shelar yaki da Palastinawa da kuma laifukan yaki sannan ta bukaci Hukumomin na haramtacciyar kasar Isra’ila da su tsaida wannan ta'asa cikin gaggawa.
A makun da ya gabata ne , piraministan haramcecciyar kasar Isra'ila Banjamin Natan yahu ya bada umarnin rusa gidanjen Palastinawa da suke adawa da manufofin Isra'ila.inda a ranar laraban da ta gabata Sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka rusa gidan Shahid AbdulShaludi wanda ya kai hari da motar sa ga wasu yahudawa a Baitul-mugadas.
A tunanin Natan Yahu yin hakan shi ne dauka fansa ga iyalansa da kuma hana abkuwar irin wannan hari a nan gaba.
2615222