IQNA

Ana Shirin Bude Wata Hanya Yanar Gizo Ta Sadarwa Ta Facebook Na Musulunci

20:07 - December 07, 2014
Lambar Labari: 2616182
Bangaren kasa da kasa, nan da shekara mai zuwa ta 2015 za a bude wata sabuwar hanya ta sadarwa ta yanar gizo internet ta facebook mai suna Salam World wadda za ta mayar da hankali ga matasa musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ifr.fr cewa a cikin shekara mai zuwa ta 2015 za a bude wata sabuwar hanya ta sadarwa ta yanar gizo internet ta facebook wadda ake kira da Salam World wadda za ta mayar da hankali domin wayar da kan matasa.

Bayanin ya ci gaba da cewa a tashin farko wannan shafi zai fara da karbar mutane miliyan 50, kafin daga bisani ya kara fadada ayyuaknsa zuwa wani adadi, kuma aikinsa zai zama na fadakar da matasa ne da kuma yada al'adu na muslunci kamar dai yadda masu shirin suka sanar, sannan kuma sun zabi birnin Istanbul na kasar Turkiya ya zama wurin da za su kafa cibiyarssu domin gudanar da wannan aiki a cikin shekara ta 2015.

Shafin zai rika karbar abokai ne musulmi amma kuma ga wadanda ba musulmi da suke gudanar da bincike kan muslunci za su iya amfana da wannan shafi domin sanin abubuwa da dama da suke bukata dangane da addinin muslunci, kuma za a basu dukkanin taimakon da suke bukata domin gudanar da binciken.

2615591

Abubuwan Da Ya Shafa: shafi
captcha