Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NBCNEWS cewa, mutumin wanda shi ne ake tuhumarsa da kashe wani matashi musulmi bai yi wata-wara ba wajen bayyana kanda da cewa shi mai matukar gaba da musulmi da kuma addinin muslunci a kasar ta Amurka da duk inda suke.
A jiya daruruwan abokai da kuma dangin akai gurley bakar fata dan kasar Amurka da wani dansanda ya harbe, sun gudanar da janazarsa jiya a mahaifarsa da ke yankin bruklin na kasar.
Rahotanni daga kasar sun ce sun habarta cewa an gudanar da janazar akai gurley ne a majami'ar brown Memorial inda mahalarta janazar suka nuna alhininsu da fushinsu kan kisan da aka yi masa ba tare da wani laifi ba, duk kuwa da cewa rundunar 'yan sandan Amurka ta bayyana cewa an harbe shi ne bisa kure.
A ranar ashirin ga watan Nuwamban da ya gabata ne dan sandan ya harbe gurley wanda ba ya dauke da makami, lamarin da ya kara kunna wutar rikicin kin gwamnati a tsakanin al'ummar kasar, musamman ma bakaken fata, wadanda suke ganin cewa jami'an 'yan sanda fararen fata suna cin zarafinsu saboda launin fatarsu.
A cikin 'yan kwanakin nan ne dai kutu ta sallami wasu 'yan sanda farar fata da suka kashe wasu bakaken fata har lahira, lamarin da ya jawo zanga-zanga a fadin kasar mafita cikin sheakru hamsin da suka gabata.