Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahabrata cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar ta talabijin ta Al-lama cewa, kotu a kasar Masar ya yanke hukuncin kisa kan wasu ‘yan kungiyar yan uwa musulmi su hudu bisa tuhumarsu da kashe jami’an tsaro a a ranar 28 ga watan Fabrairu a lokacin juyin juya hali wanda ya kai ga tumbuke gwamnatin kama karya.
Wannan kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan magoya bayan kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood guda hudu a jiya Lahadi a birnin Alkahira na kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan wasu ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood magoya bayan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi bayan da tace ta same su da hannu dumu-dumu a aiwatar da kisan gilla, tunzura mutane kan aiwatar da kisa, mallakar makamai da harsasai ba a kan doka ba da kuma shiga cikin kungiyar ‘yan bindiga domin gudanar da ayyukan wuce gona da iri kan al’umma.
A makon da ya gabata ma an yanke wani hukuncin kan mutane 188 bisa zargin kashe yan sanda 13, daga cikinsu har Muhammad bade shugaban kungiyar a watan Agustan 2013, mutanen hudu da aka yanke musu hukuncin kisa a jiya Lahadi suna daga cikin ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulmi da ake zargi da hannu a kisan jama’ar da suka gudanar da zanga-zanga ta nuna kin jinin gwamnatin Muhammad Morsi tare da yin ruwan duwatsu kan babbar cibiyar kungiyar ‘yan uwa musulmi suna neman Morsi da ya yi murabus daga kan shugabancin Masar a ranar 30 ga watan Yunin shekara ta 2013 da ta gabata.