IQNA

Ana Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Mai Tsarki A Moroco

23:13 - December 09, 2014
Lambar Labari: 2617123
Bangaren kasa da aksa, ana gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar morocco da ta hada da tajwidi da tartili.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manarah cewa, tun a jiya ne aka fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar morocco da ta hada da tajwidi da tartilin karatun.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na 10 da ake gudanar da irin wannan gasa wadda tak samun halartar makaranta da mahardata daga sassa na kasar wadanda suke gudanar da karatu a bangaren harda, da kuma tajwidi da kira'a kawai, kawai kamar dai yadda bayanin ya tabbatar.

Ma'aikatar kula da harkokin ala'adu a kasar ce dai a bangaren kula da harkokin kur'ani ta dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da wannan babbar gasa, da dama daga cikin masu halartar gasar dai suna ganin ci gaba da aiwatar da ita a irin wannan yanayi na da matukar muhimamnci, musamman idan aka kalli tasirin haka a tsakanin matasa.

Kasar Moroco dai tana da cikin kasashen larabawan yankin arewacin nahiyar da suke mayar da hankali matuka ga harkokin karatu da kuma harder kur'ani har da shirya gasarsa.

2616735

Abubuwan Da Ya Shafa: Moroco
captcha