IQNA

Wani Makarancin Kur'ani Da Kasar Moroco Ya yi Daya A Gasar Kur'ani Ta Internet

22:56 - December 11, 2014
Lambar Labari: 2617671
Bangaren kasa da kasa, Hamza Abdulfattah Warrash wani makarancin kur'ani mai tsarki dan kasar Moroco ya zo a matsayi na farko a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar yanar gizo da aka gudanar a Bahrain a wannan mako.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na klamfanin dilalncin labaran kasar Barain cewa, wani makarancin kur'ani mai tsarki dan kasar Moroco mai suna Hamza Abdulfattah warrash ya zo na daya a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar yanar gizo wato internet da aka gudanar a Bahrain a wannan mako tare da halartar da dama cikin makaranta na kasa da kasa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan makaranci dai ya nuna kwazo matuka, ta yadda ya samu damar kaiwa ga wannan matsayi a tsakanin daruruwan makaranta, duk kuwa da cewa an gudanar da alkalanci sahihi domin tantancen kwazon kowane daga cikinsu da kuma cancantarsa, amma duk da haka babu inda ya gaza.

Kasar Moroco dai na daga cikin kasashen da suke bayar da himma matuka a bangaren karatun kur'ani, duk kuwa da cewa kokarin yana komawa ne ga himmar al'aummar kasar da suke da tsohon tarihi wajen karatu da kuma harder kur'ani mai tsarki.

Yanzu haka dai wannan makaranci ya karbi kyautuka masu tarin yawa daga babbar cibiyar da ta dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da wannan gasa ta kur'ani ta hanayar yanar gizo,a  amtasyi na kasa da kasa.

2617537

Abubuwan Da Ya Shafa: Moroco
captcha