Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-alam cewa, masu kula da lamarin ziyara a kasar Iraki sun tabbatar da cewa adadin masu ziyarar arba'in na Imam Hussain (AS) a wannan shekara ya kai mutane miliyan 19 kuma addain na karuwa wanda hakan ke nufin zai haura matuka.
Bisa ga bayanin akwai motoci 1400 da kuma ma'aikatansu 9600 da suke gudanar da aikin hidima ga miliyoyin mutane da suke gudanar da tarukan arba'in na shahadar Imam Hussain (AS) a hubbarensa da ke birnin Karbala na kasar Iraki.
Bayanai daga birnin na Karbala na cewa fiye da mutan emiliyan 19 suka isa birnin daga sassa na kasar Iraki da kuma kasashen ketare, domin halartar tarukan na ranar 40 na shahadar Imam Hussain (AS) a hubbaren nasa, hakan na wakana ne duk da irin barazanar ta'addanci da kasar ke fuskanta daga 'yan ta'adda masu da'awar jihadi ko kafa a bin da suke kira daular Islama.
Sai dai daga nasu bangaren jami'an tsaron kasar ta Iraki sun dauki kwararn matakan tsaro a ciki da wajen birnin na Karbala, domin kare rayukan masu gudanar da tarukan, inda runduna hadin gwiwa tsakanin sojoji da 'yan sanda ta saka jami'anta fiye da dubu talatin suna gudanar da ayyukan tsaro a taron na karbala mai alfarma.