IQNA

Musulmin kasar Malawi Sun Jaddada Wajabcin Koyar Da Kur'ani Tun Daga Kuruciya

22:36 - December 15, 2014
Lambar Labari: 2618812
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Malawi sun jaddada wajabcin koyar yaransu karatun kur'ani mai tsarki tun daga lokacin kuruciya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nyastimes cewa, a wani zaman da suka gudanar malaman mabiya addinin muslunci a kasar Malawi da ke yammacin nahiyar sun jaddada wajabcin koyar yaransu karatun kur'ani mai tsarki tun daga lokacin kuruciya domin hakan ya zama fitila mai haskaka musu.

Bayanin ya ci gaba da cewa musulmin kasar Malwi na daga cikin musulmin kasashen yammacin nahiyar Afirka da ke bayar muhimamnci matuka wajen koyar da kur'ani mai tsarki a makarantunsu, wanda hakan ya sanya su suke taka gagarumar rawa wajen hidima ga wannan littafi mai tsarki, wanda hakan ya hada hard a lokutan gasar karatu da hardarsa a kasashen duniya.

Wannan bayani ya zo a daidai lokacin kammala wani taron addini wanda ya hada malamai masu koyar da karatu da harder kur'ani a makarantu mallakin mabiya  addinin muslunci da suka zo daga yankuna daba-daban na kasar, inda kowa ya gabatar da ra'ayinsa da kuma shawar dangane da yadda za a kara habbaka harkar kr'ani mai tsarki a kasar.

Adadin musulmin kasar Malawi dai ya kai kashi 36 cikin dari na mutanen kasar wadanda adadinsu ya kai miliyan 16 bisa kididdigar baya bayan nan.

2618430

Abubuwan Da Ya Shafa: malawi
captcha