Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na jaridar Al-mostaqhbal ta kasar Lebanon cewa, Monesniyor wanda shi ne babban sakataren bangaren kula da harkokin ziyara na fadar Vatican ya bayyana tarukan arbain na Imam Hussain da cewa wannan ne ke bayyana hakikanin addinin muslunci da kuma koyarsa ta zaman lafiya da 'yan uwantaka.
Dangane da wannan nasarar da aka samu a tarukan na bana firayi ministan iraki ya godewa daidaikun mutanen kasar Iraqi, musamman jami’an tsaron kasar wadanda suka hada da yansanda, sojoji da masu sa kai. Ibada ya kara da cewa, nasara juyayin arba’in na shugaban shahidai wata nasara ce babban ga jami’an tsaron kasar Iraqi, wadanda a halin yanzu suke fafatawa da mayakan yan ta’adda a wasu sassa a cikin kasar.
Har’ila yau ya godewa miliyoyin masu ziyara daga ciki da wajen kasar kan bada hadin kai da suka yi ga jami’an tsaro na gwamnati da kuma na masu sa kai, a lokacin wannan taron. Amma duk da haka gwamnatin kasar ta bayyana cewa, matakan tsaron da aka dauka a lokacin wannan taron zasu ci gaba har zuwa wani mako guda don tabbatar da cewa, ba’a bawa yan ta’adda daman a cutar da mutane bayan wannan nasarar ba.
Duk da cewa, a bana an gudanar da taron arba’in a cikin yanayi na barazanar hare hare daga kungiyar yan ta'adda wacce take mamaye da wasu yankuna na kasar Iraqi a halin yanzu, amma yawan masu ziyara ya dara na bara, da muatane fiye da miliyon biyu.
Jamhuriyar Musulunci ta dai tana kan gaba da yawan masu ziyara daga kasashen waje, inda yawan Iraniyawan da suka je makokin arba’in a bana ya dara miliyon daya da rabi.
2620318