IQNA

Kungiyar ISESCO Ta Yi Allawai Da Kisan Gilla Kan Dalibai A Kasar Pakistan

15:58 - December 17, 2014
Lambar Labari: 2620669
Bangaren kasa da kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasahen musulmi ISESCO ta yi kakkausar da yin Allawadai da kisan gillar da wasu 'yan kungiyar Taliban suka yi wa yara 'yan makaranta ajiya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na INA cewa, Iyad Amin Madani babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasahen musulmi ta yi kakkausar da yin Allawadai da kisan gillar da wasu 'yan kungiyar Taliban suka yi wa yara 'yan makaranta  a garin Bishawur.
Rahotanni daga kasar ta Pakistan sun bayyana cewar alal akalla mutane 135 ne mafiya yawansu kananan yara suka rasa rayukansu kana wasu sama da114  dari kuma suka sami raunuka sakamakon wani hari da mayakan Taliban suka kai wata makaranta da ke yankin Peshawar na kasar ta Pakistan.

Shaidun gani da ido sun shaida wa kamfanin dillancin labaran cewa lamarin ya faro ne bayan da mayakan Taliban din suka fasa wani abu mai kara a makaranta kana kuma wasu ‘yan kungiyar su shida cikin kayan jami’an tsaro suka shiga makarantar da bude wuta kan ‘yan makarantar wadanda wasu aka ce ba su wuce shekaru a duniya ba.
Kungiyar Taliban ta kasar Pakistan da ake kira da  Pakistan ta ce ita ce ta kai wannan hari a matsayin mai da martani ga hare-haren da ake kai wa mayakansu a Arewacin Waziristan da kuma lardin Khyber. Jami’an tsaron Pakistan din dai sun ce sun hallaka dukkanin mutane shidan da suka kai wannan harin.
Jami’an kasashen duniya daban-daban bugu da kari kan na cibiyoyin kasa da kasa suna ci gaba da Allah wadai da wannan danyen aiki wanda aka ce shi ne irin sa na farko da kasar Pakistan din ta fuskanta cikin shekaru bakwai din da suka gabata.
2620323

Abubuwan Da Ya Shafa: pakistan
captcha