IQNA

Azhar Ta Ce Garkuwa Da Mutane A Kasar Australia Ba Shi Da Aalaka Da Musulunci

16:01 - December 17, 2014
Lambar Labari: 2620673
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar muslunci ta Azhar a kasar Masar ta bayyana garkuwa da aka yi da farareren hula a birnin Sydney na kasar Australia da cewa ba shi da wata laka da addinin muslunci aiki ne na ta'addanci kawai.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almujiz cewa, cibiyar muslunci ta Azhar a kasar Masar ta bayyana garkuwa da aka yi da farareren hula a birnin Sydney na kasar Australia da cewa ba shi da wata laka da addinin muslunci aiki ne na ta'addanci abin yin Allawadai.
Ita ma a nata bangaren jamhuriyar Musulunci ta yi Allah wadai da garkuwa da mutane da wani dan bindiga ya yi a birnin Sydney na kasar Australiya, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi tofin Allah tsine kan garkuwa da mutane da wani dan bindiga ya yi a wani wajen shan coffe da ke birnin tana mai jaddada cewar amfani da matakin wuce gona da iri kan jama’a tare da tada hankalin mutane da tsoratar da su da sunan addinin Musulunci, addinin da yake matsayin addini na rahama da jin kai ga talikai lamari ne da ba zai taba yiyuwa a jingina shi da koyarwar addini ko dabi’ar dan adam.

An  dai kawo karshen garkuwar da mutum dan kasar Australia ya yi da mutane hamsin a birnin Sydney bayan kashe shi har lahira, sakamakon kutsa kai da jami'an tsaron kasar suka yi a cikin wurin tare da bude masa wuta,  majiyoyin tsaron kasar sun ce mutumin wanda yake dauke da akidun wahabiyanci da takfiriyya na kungiyoyin da ke da alaka da alkaida.

Ya kuma tsare mutanen ne tun jijjifin safiyar Litinin a wani dakin shan shayi da Kahwa a birnin Sydney, inda yake dauke da muggan makamai da kuma bakatar tuta mai kama da tutar 'yan ta'addan ISIS masu da'awar jihadi.
Cibiyoyin addinin muslunci fiye da arbain ne  akasar suka fitar da bayani a yau na yin Allawadai da wannan aiki, tare da bayyana cewa irin wanann halayya ta saba wa koyarwar addinin muslunci, tare da yin Allawadai da malaman da ke wanke kwakwalen matasa musulmi, tare da tunzura su zuwa ga ayyukan ta'addanci.
2619098

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha