IQNA

Ta’addanci Ba Shi Da Wata Alaka Da Addinin Musunci Ko Kodan

15:19 - December 21, 2014
Lambar Labari: 2623649
Bangaren kasa da kasa, dan majalisar dokokin kasar Rasha ya bayyana cewa ayyukan ta’addanci da ake gani daga wasu masu karkataccen tunani bas hi da wata alaka da addinin muslunci balanta ma masu aikata shi.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Russia Today cewa, Shamsil Saralif wanda dan majalisar dokokin kasar Rasha ne yana bayyana cewa irin ayyukan ta’addanci da ake gani a halin yanzu a duniya daga wasu masu batattun mutane marassa tunani ba shi da wata alaka da addinin muslunci kuma masu yin hakan abs u wakiltarsa.
Shi kuwa a nasa bangaren Shugaban jamhuriyar muslunci ya kirayi kasashen yankin gabas ta tsakiya ne da su hada karfi da karfe domin kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin baki daya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron kasa da kasa da aka bude yau a babban birnin kasar, kan yaki da ayyukan ta'addanci da tsatsauran ra'ayi da wuce gona da iri, ya ci gaba da cewa Iran ta gabatar da daftarin kudiri a majalisar dinkin duniya kan batun yaki da ta'addanci a duniya, kuma kasashen duniya suka lale marhabin da hakan.
Kuma a cewarsa hakan ya yi tasiri a sauran yankuna na duniya, in ban da yankin gabas ta tsakiya, wanda hakan ke bukatar aikin hadin gwiwa tsakanin dukkanin kasahen yankin baki daya, tare da kiran kasashen larabawa na yankin da ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci da sunan addini da su canja shawara.

Babbar manufar taron wanda ke samun halaratr wakilai daga kasashen duniya daban-daban, ita ce tattauna hanyoyin da ya kamata  abi domin magance tsatsauran ra'ayi wanda ke kai ga haddasa ta'addanci, ta hanyar wayar da kai da ilmantarwa musamman ga matasa na kasashen musulmi.
2623174

Abubuwan Da Ya Shafa: rasha
captcha